logo

HAUSA

Babban hafsan sojojin Najeriya ya ba da umarnin farauto wadanda suka kaiwa jirgin kasa hari

2022-03-30 09:50:24 CMG Hausa

Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya Faruk Yahaya, ya ba da umarnin farauto wadanda suka kai hari kan jirgin kasan nan da ya tashi daga birnin Abuja zuwa jihar Kaduna a ranar Litinin. Yahaya wanda ya bayyana umarnin a jiya Talata a jihar Kaduna dake arewa maso yammacin kasar, ya bukaci sojoji da su hanzarta ayyukan sintiri, da gano wadanda aka yi garkuwa da su, tare da tantance cikakken yanayin da harin ya wakana.

Daga nan sai ya jaddada aniyar rundunar sojojin Najeriya, ta tabbatar da ganin sun murkushe ’yan fashin daji, da sauran nau’o’in laifuka dake addabar ’yan kasar.

A nasa bangare, kwamishinan cikin gida da harkokin tsaro a jihar Kaduna Samuel Aruwan ya tabbatar da rasuwar fasinjoji 8 dake cikin jirgin da maharan suka yiwa kwantan bauna, inda ya ce akwai wasu karin mutane 26 da suka jikkata yayin harin.

Shi ma babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ta bakin kakakin sa Stéphane Dujarric, ya yi Allah wadai da harin da ’yan bindiga suka kai filin jirgin sama na jihar Kaduna, da kuma harin jirgin kasa duka dai a jihar, lamarin da ya haifar da rasuwar mutane da jikkatar wasu, da sace karin wasu mutane.

Stéphane Dujarric, ya ce babban magatakardar MDDr ya bukaci mahukuntan Najeriya da su yi duk mai yiwuwa, wajen ganowa da kuma gabatar da wadanda suka aikata wannan ta’asa gaban kuliya. Ya kuma jaddada goyon bayan MDD ga gwamnati da al’ummar Najeriya, a yakin da suke yi da ayyukan ta’addanci, da tsattsauran ra’ayi, da sauran manyan laifuka.  (Saminu)