logo

HAUSA

Najeriya ta dakatar da zirga-zirgar jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna sakamakon harin da aka kai

2022-03-29 20:33:52 CMG Hausa

Hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Najeriya (NRC ) ta dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa tsakanin Abuja, babban birnin kasar da kuma birnin Kaduna dake arewacin kasar na wani dan lokaci, sakamakon wasu dalilai, biyo bayan wani harin da wasu 'yan bindiga suka kai kan wani jirgin kasa a kan hanyar ranar Litinin da dare.(Ibrahim)