logo

HAUSA

OCHA ya nuna damuwa game da barkewar tashin hankali a yankin Ituri na janhuriyar dimokaradiyyar Congo

2022-03-29 11:17:28 CMG Hausa

Ofishin MDD mai tsara ayyukan jin kai ko OCHA, ya bayyana matukar damuwa game da sake tabarbarewar yanayin tsaro da jin kai a lardin Ituri na jamhuriyar dimokuradiyyar Congo.

OCHA ya bayyana cewa, daga farkon shekarar bana zuwa yanzu, barkewar tashe-tashen hankula a lardin na gabashin jamhuriyar dimokuradiyyar Congo, ya sabbaba kisan fararen hula kimanin 400, tare da raba wasu sama da 83,000 da gidajen su.

Kaza lika ofishin ya ce, cikin mako na 2 na watan Maris din nan kadai, adadin fararen hula da aka hallaka a Ituri, ya kai kusan mutum 80. Har ila yau, jami’an ba da agajin jin kai sun lura da karuwar hare hare kan fararen hula da suka riga suka tserewa gidajen su, da ma a yankunan da wannan rukuni na al’umma ke samun mafaka. Kana akwai mutane 488,000 da suka fada tasku, sakamakon lalata cibiyoyin kula da lafiya, da makarantu a lardin na Ituri, tun daga shekarar 2021 kawo yanzu.

Tashe tashen hankula sun kuma dakile damar kai agaji, tare da haifar da jinkirin ayyukan, har ma da sauya wuraren gudanar da su.

Bisa kiyasi, akwai fararen hular Ituri da yawan su ya kai miliyan 1.9, da suka rabu da gidajen su, adadin da ya kai kaso 1 cikin 3 na daukacin ’yan kasar masu gujewa matsugunnansu. A daya hannun kuma, akwai ’yan kasar kusan miliyan 3, sama da rabin al’ummar Iturin dake fama da karancin abinci.  (Saminu)