Muhammad Aminu Saifullahi: Ina kira ga matasan Najeriya su kara hadin-kai don raya kasarsu tare
2022-03-29 14:28:01 CRI
Muhammad Aminu Saifullahi, dan asalin Sokoton Najeriya, yanzu haka yana karatun digiri na biyu a fannin nazarin sinadarai wato Chemical Engineering a wata jami’a dake birnin Huainan na lardin Anhui dake kasar Sin.
A yayin zantawarsa da Murtala Zhang, malam Saif ya bayyana ra’ayinsa kan bambancin yanayin karatu tsakanin Najeriya da kasar Sin. Kuma a cewarsa, a fannin karatun da yake nazari yanzu, wato amfani da bakin gawayi don samar da wutar lantarki, Najeriya da Sin na da wurare da dama na fadada hadin-gwiwarsu.
A karshe, malam Saif ya yi kira ga matasan Najeriya su tashi tsaye don kara hadin-gwiwa, a wani kokari na raya kasarsu tare. (Murtala Zhang)