logo

HAUSA

Zhoigar da Yangzom furannin galsang ne masu tsaron yankin iyakar kasar Sin

2022-03-29 11:15:27 CMG

 

Zhoigar da Yangzom ‘yan uwan juna ne dake zaune a garin Yumai na gundumar Lhunze, dake Shannan, wani birni dake yankin Tibet mai cin gashsin kansa na kudu maso yammacin kasar Sin. Tun daga shekarun 1960, ‘yan matan ‘yan kabilar Tibet ke bin sawun mahaifinsu, Sangye Chupa, inda suke kare yankunan iyaka na kudu maso yammacin kasar  Sin. Zuri’o’i 3 na wannan iyalin makiyaya, na daga tutar kasar Sin yayin da suke sintiri a yankunan iyaka. Labarin wannan iyali, ya ba mutane da dama a kasar Sin mamaki.

Yumai wani gari ne mai nisa dake boye a kasan tsaunikan Himalays. Yana yankin iyakar Sin da Indiya. A lokacin da aka kafa Yumai a matsayin gari a shekarar 1959, Sangye Chupa ne ya zama shugaba na farko. Bayan shekaru 30, galibin mazaunan sun kaura zuwa wasu wurare saboda wahalar fita daga Yumai zuwa wuraren dake wajen tsaunikan. Gidan iyalin Sangye Chupa, shi ne ke zaman ofishin gwamnatin Yumai.

Rayuwa a yankin tsaunika na da matukar wahala a wancan lokaci. Yumai ya kasance kamar wani kebabben wuri, a kowanne lokacin hunturu, tsakanin Nuwamba da Mayu, a wancan lokaci, dusar kankara mai yawa ne ke lullube garin. Amma duk da haka, Sangye Chupa ya dage sai ya zauna a garin.

An ruwaito Songye Chupa na cewa: “Idan iyalina ma suka bar garin, to wa zai kare iyakar kasarmu? Mutanen da ba a san adadinsu ba ne suka sadaukar da kansu wajen ‘yantar da Tibet. Wahalar da za mu sha ba za ta taba kama kafar tasu ba.” Zhoigar da Yangzom na iya tuna lokacin da mahaifinsu ke furta wadannan kalamai, a lokacin suna kanana.

Sangye Chupa ya taba sayen wasu yadudduka biyu, daya mai launin ja dayan kuma rawaya. Zhoigar da Yangzom sun yi ta tunanin me mahaifinsu zai yi da wadancan yaduddukan. Bayan sun ci abincin dare, ‘yan matan na kallo, mahaifinsu ya yayyanka yaduddukan inda ya dinke su zuwa tutar kasar Sin, tuta mai launin ja da taurari 5 masu launin rawaya. Sangye Chupa ya kuma gaya wa yaransu cewa, “Wannan tutar kasarmu, abu ne mafi daraja na al’ummar Sinawa”. Daga lokacin, an fara daga tukar kasar Sin a gari Yumai.

Bayan mutuwar matar Sangye Chupa, a lokacin hunturu na shekarar 1978, ya ci gaba da zama da ‘yan matan biyu a Yumai, inda ya tura karamin dansa wajen garin domin koyon aikin likita. Tun daga sannan, Yumai ya zama gari mai mazauna 3, wato Sangye Chupa da Zhoigar da Yangzom.

“A wani lokacin, rayuwa na da wahala, akwai kuma kadaici, amma muna da goyon bayan kasarmu. ‘Yan gidanmu cike suke da fata na gari”, cewar Yangzom. Zhoigar ta kara da cewa, tana yawan tuna abun da mahaifinta ke cewa, “Yumai yankin iyakar kasarmu ne. Ya kamata mu tsayar da tutarmu a yankin, inda muka rayu daga zuri’a zuwa zuri’a.”

Bayan Sangye Chupa ya yi ritaya a 1988, Zhoigar ce ta gaje shi a matsayin shugabar Yumai, inda Yangzom ta zama mataimakiyarta. A 1996, gundumar Lhunze ta fara tura jami’ai domin su yi aiki a Yumai, daga nan ne kuma karamin garin dake boye cikin tsaunika da dusar kankara, ya sauya daga gari mai mazauna 3.

A shekarar 1997, wasu kafafen yada labarai suka bayar da rahoto game da iyalin Sangye Chupa na kare yankunan iyakar Yumai. Wannan iyalin na Tibet, sun burge mutane da dama da suka ji labarin wannan gari mai mazauna 3. Wasu mutane ma har wasiku suka rubutawa Zhoigar da Yangzom, domin bayyana kaunarsu gare su. Sai dai, wadannan ‘yan uwa, sun yi wa mahaifinsu alkawarin samar da iyalinsu a Yumai. Yangzom ta yi aure lokacin da take da shekaru 27, yayin da Zhoigar ta yi nata a shekaru 35. “ Yumai ce mahaifarmu, kasarmu kuma Sin. Ni da ‘yar uwata, ba mu taba kokonta zama domin taimakawa kare wannan wuri ba,” cewar Yangzom.

Tun daga 1978, a lokacin da Sin ta fara aiwatar da manufar bude kofa ga wajen da yin gyare-gyare a gida, yankin Tibet mai cin gashin kansa ya samu taimako sosai daga gwamnatin tsakiya a kokarinta na raya kasa. An ware kudi na musammam a farkon shekarun 1990, domin inganta ginin ababen more rayuwa a Yumai. An gina sabon ofishin gwamnati. Sannan an gina tashar samar da lantarki da kuma tashar samun siginar tauraron dan Adam. Iyalin Sangye Chupa ma, sun kaura zuwa sabon gida da aka kawata da talabijin da fitilun lantarki.

Babban burin Sangye Chupa ya cika ne a watan Satumban 2001, a lokacin da aka kammala ginin titin da ya hada Yumai da yankunan wajen tsaunikan. Sangye Chupa, a lokacin yana da shekaru 77, ya tafi Lhasa a cikin mota. Ita kuwa Zhoigar, ta yi bulaguro mai nisa ne, inda ta je Shaoshan, na lardin Hunan dake tsakiyar kasar Sin, domin ziyartar tsohon gidan Marigayi Mao Zedong. Zuwa karshen 2001, iyalai 5 da suka kunshi mutane 25 ne ke zaune a Yumai. Karamin garin ya bude ofishin ‘yan sanda da makarantar firamare. A lokacin hunturu na wannan shekara, Sangye Chupa ya rasu bayan ganin cikar burinsa. Kalamansa na karshe ga yaransa da mazaunan Yumai su ne, “ A Yumai kaka da kakanninmu suka rayu, kuma ita ce mahaifarmu, ku kare duk wata ciyawa da bishiya dake tufuwa a wannan wuri.”  

An samu sauye-sauye da dama a Yumai cikin gomman shekarun da suka gabata. Zuwa karshen shekarar 2018, iyalai 9, ciki har da na Zhoigar da Yangzom, sun kaura zuwa sabbin gidaje. ‘Yan uwan sun fahimci cewa, ba don kulawa ta musammam da kwamitin tsakiya na JKS ta shafe shekaru tana ba yankin ba, da ba za su samu rayuwa mai dadi da suke morewa yanzu ba. Don haka, Zhoigar da Yangzom, suka rubuta wasika zuwa ga Xi Jinping, sakatare janar na kwamitin tsakiya na JKS kuma shugaban kasar Sin, inda suka bayyana muhimman sauye-sauyen da Yumai ta samu. Sun yi mamaki da suka samu amsa daga shugaba Xi a ranar 29 ga watan Oktoban 2017. Shugaba Xi ya karfafa musu gwiwar ba makiyaya kwarin gwiwar zama a yankin na iyaka, a cewarsa, kamar fure galsang, sannan su zama masu tsaron iyakar kasar Sin da samar da farin ciki a garin. ‘Yan uwan sun ce samun wasika daga Shugaba Xi, abu ne da suke alfahari da shi a rayuwarsu.

Bayan mutuwar mahaifinsu, Zhoigar da Yangzom, da iyalansu, sun ci gaba da zama a Yumai domin kare yankin na kan iyaka. Suna tatsar nonon shanu da kayan kwalam na gargajiya da saka kwando da sauransu. Makiyayan na rayuwa mai sauki a tsakanin tsaunikan. Zhoigar na da ‘ya’ya mata 3, Yangzom kuma tana da namiji daya da mace daya. Yaran sun yi karatu ne a wajen garin.

Dan Yangzom, Soinam Toinzhub, ya kammala kwaleji a 2017, inda ya zama mutum na farko da ya kammala kwaleji a Yumai. Daga baya, ya rubuta jarrabawar neman aikin gwamnati. “Mahaifiyata da goggona sun cika burin kakana na zama a Yumai. A yanzu, ina aiki da burin mahaifiyata, kuma zan ci gaba da kare mahaifarmu,” cewar Soinam Toinzhub.

Babbar diyar Zhoigar, Pasang Zhoigar, ta kammala kwaleji a shekarar 2019. Yanzu haka tana aiki a matsayin jami’ar da ta kware kan farfado da kauye a Niulintang, wani kauyen Yumai. Tana son koyi da kakanta da mahaifiyarta da kuma goggonta, kuma tana son raya wannan ruhi na kishin kasa da kuma kare yankin iyakar. “har yanzu Yumai na da damarmakin samun karin ci gaba. Zan sauke nauyin dake wuyana, kuma zan taimakawa ‘yan uwana na kauyen wajen samun ci gaba a garimu,” cewar Pasang Zhoigar.

Kanwarta, Chemi Zhoigar, diyar Zhoigar ta biyu, ita ma ta koma Yumai bayan ta kammala karatu. Zhoigar da Yangzom na ganin yana da muhimmanci yaransu su samu ilimi mai inganci, ta yadda za su taimaka wajen gina kyakkyawar makoma ga Yumai.

“Bayan mun fita mun ga yadda duniya take da kyau, mun kara kaunar yankinmu mai kyau da muka taso,” cewar Zhoigar. Ita da Yangzom, na rike da akidar cewa, aikin iyalinsu shi ne, jagorantar mazauna domin zama a yankin, da kare shi da kuma bunkasa ci gaba mai dorewa a Yumai.