logo

HAUSA

Kasar Sin tana taimakawa al'ummar Afganistan fita daga cikin mawuyacin hali da ayyuka a zahiri

2022-03-29 19:37:10 CMG Hausa

Dan majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, zai jagoranci taron ministocin harkokin wajen kasashen dake makwaftaka da kasar Afganistan karo na uku a birnin Tunxi na lardin Anhui, inda za su tattauna kan "shirin da kasashe makwabtan ke da shi" don yin hadi gwiwa wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar Afghanistan, da goyon baya da taimakawa jama’ar Afghanistan a mataki na gaba. A ziyararsa ta baya-bayan da ya kammala a kasashe da dama na yankin Asiya, Afghanistan shi ne muhimmin zango. Wadannan ayyuka sun nuna cewa, kasar Sin tana kokari matuka wajen sake gina Afganistan cikin lumana, kuma tana fatan kasar da yaki ya daidaita, za ta farfado nan ba da jimawa ba.

Koma dai daga bangaren dake zama "zuciyar Asiya", ko kuma ta mahangar "masu bibiyan yakin Afghanistan da yaki da ta'addanci a duniya, halin da ake ciki a Afganistan yana da alaka da tsaro da zaman lafiyar yankin da ma duniya baki daya, kuma ba za a iya yin watsi da shi ba, saboda irin abubuwan da suka faru kamar rikicin Ukraine. (Ibrahim)