logo

HAUSA

Yin barci da wuri da kuma farka da wuri suna kare mutane daga kamuwa da ciwon bakin ciki

2022-03-29 09:22:23 CMG Hausa

  


Alkaluman hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO sun nuna cewa, ciwon bakin ciki, wani nau’in ciwo ne na tunani wanda ake yawan kamuwa da ita. Yanzu mutane kimanin miliyan 264 suna fama da ciwon a duk duniya baki daya. Wani sabon nazari na kasar Amurka ya shaida cewa, idan mutane sun yi barci awa daya kafin lokacin barcin da suka saba yi, to, zai rage musu yiwuwar kamuwa da ciwon bakin ciki da kaso 23 cikin dari.

A baya, akwai nazarin da ya nuna cewa, duk tsawon lokacin da aka dauka wajen yin barci, wadanda suka saba da yin barci a makare da dare sun fi fuskantar yiwuwar kamuwa da ciwon bakin ciki, har sau biyu, gwargwadon wadanda suka saba da yin barci da wuri da kuma farkawa da wuri.

Masu nazari daga hukumar nazari ta Broad na Amurka sun bibiyi  mutane kimanin dubu 840 dangane da yadda suka yi barci, tare da kimanta sauye-sauyen da suka samu a kwayoyin halitta, wadanda kila za su ba da tasiri kan yadda suka yi barci da aiki. Binciken ya nuna cewa, a cikin wadannan mutane dubu 840, wasu kaso 33 cikin dari sun saba da yin barci da wuri da kuma farkawa da wuri, yayin da wasu kaso 9 cikin dari suka saba da yin barci a makare da dare. Galibi dai sun saba da yin barci da daddare da karfe 11, yayin da su kan farka daga barci da karfe 6 na safe.

Masu nazarin sun kuma yi bibiyi tarihin wadannan mutane dangane da samun jinya, tare da gudanar da bincike kan ko sun kamu da ciwon bakin ciki ko a’a. Sun gano cewa, wadanda suka saba da yin barci da wuri da kuma farkawa da wuri, ba sa fuskantar babbar barazanar kamuwa da ciwon bakin ciki. Amma idan wadanda suka saba da yin barci a makare a dare suka yi barcin awa daya kafin lokacin da suka saba, to, zai rage musu barazanar kamuwa da ciwon bakin ciki da kaso 23 cikin dari. Alal misali, wani ya saba da yin barci da karfe 1 na sassafe, idan ya fara yin barci da karfe 12 na dadare, wato awa guda kafin lokacin da ya saba, bai rage ko tsawaita lokacin barci ba, to, zai rage masa barazanar kamuwa da ciwon bakin ciki har kaso 23 cikin dari.

A baya wasu masu nazari sun yi nuni da cewa, wadanda suka saba da yin barci da wuri da kuma farkawa da wuri suna kara samun hasken rana a rana, lamarin da ya haifar da karuwar yawan sinadarin hormone a jikinsu, ta haka za samu sassaucin bakin cikinsu da kuma kara samun farin ciki.

Madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta da shawarar cewa, idan mutane suna son yin barci da wuri da kuma farkawa da wuri, to, zai fi kyau su taka da kafa su je aiki ko kuma su hau keke, da dare kuma su rage hasken kayayyakin laturoni na zamani, ta yadda za su samu yanayi mai dacewa da yin barci, wato a samu haske a rana, da dare kuma duhu.  (Tasallah Yuan)