logo

HAUSA

Jakadan Sin ya bukaci a dagewa Sudan takunkumi

2022-03-29 10:00:31 CMG Hausa

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Dai Bing, ya yi kira da a gaggauta dagewa kasar Sudan takunkuman da aka kakaba mata. Jami’in ya ce sakamakon ficewar dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar AU daga yankin Dafur na Sudan, mahukuntan kasar sun rungumi matakan kare fararen hula yadda ya kamata, don haka ya dace a karfafa ikonsu na wanzar da tsaro. 

Dai Bing ya kara da cewa, takunkumin hana kasar sayen makamai ya yi mummunan tasiri a fannin tabbatar da tsaron kasar, don haka ya dace kwamitin tsaron MDD, ya daidaita matakan dake kunshe cikin takunkuman da aka sanyawa kasar a kan lokaci, bisa yanayin da kasar ke ciki a halin yanzu.

Kudurin kwamitin tsaron MDD mai lamba 2620 da aka amincewa a watan da ya gabata, ya tanadi samar da mizanin daidaita takunkuman da aka sanyawa Sudan nan zuwa 31 ga watan Agusta. Don haka dai burin Sin shi ne a aiwatar da tanadin wannan kuduri yadda ya kamata.

Jami’in na Sin ya bayyana wadannan takunkumai a matsayin shinge dake dakile ci gaban kasar Sudan. Kuma a cewarsa, sau da dama takunkumai ba sa warware matsalolin da ake fuskanta, maimakon haka sai ma haifar da sabbin matsaloli, da fadada kalubalen kamfar abinci, da makamashi, da tattalin arziki, da yanayin zamantakewar al’ummar kasar.

Daga nan sai ya yi kira ga kasashen dake da ruwa da tsaki game da batun takunkuman da su sauya matsaya, tare da daukar sauran kasashe daidai da saura, su kuma yi aiki tare domin cimma moriyar juna.    (Saminu)