Kar a bar kasashen yamma su yi babakere game da batun hakkin dan Adam
2022-03-28 20:43:26 CMG Hausa
Wakilin kasar Sin Chen Xu ya yi jawabi a wajen taron majalisar hakkin dan Adam ta MDD, a kwanan baya, inda ya jaddada muhimmancin batun “samun ci gaba” a matsayin maganar da ta shafi hakkin dan Adam. Dalilin da ya sa jami’in na kasar Sin ya jaddada wannan batu, shi ne kasashen yammacin duniya su kan yi biris da burin “ neman samun ci gaba” na kasashe masu tasowa da gangan.
Yayin da suke hulda da sauran kasashe, kasashen yamma su kan dora muhimmanci kan hakkin dan Adam a fannin siyasa kawai, ba tare da lura da hakkin mutum da ya shafi tattalin arziki, da zaman al’umma, da al’adu ba. Wannan dalili ya sa kasashen yamma ke matukar daukaka batun ‘yancin furta albarkacin baki na daidaikon mutane, har ma suke kokarin kare mazanin kasar Danmark da ta wulakanta Annabi Mohammed da gangan. Yayin da a sa’i daya kuma, suna fakewa da batun “dimokuradiyya” suna saka takunkumi da tayar da yaki a kasashe irinsu Iraki, da Libya, da Afghanistan, inda suka azabtar da jama’ar wadannan kasashe sanadiyyar yaki da yunwa, ba tare da jin kunya ko tsoron Allah ba.
Haka kuma wani babban dalilin da ya sa ake samun matsaloli daban daban a duniya, shi ne yadda wasu kasashen yamma ke kokarin neman yin babakere game da maganar hakkin dan Adam, da sauran batutuwa. Wasu ‘yan kasashen yamma suna tsammanin cewa, sun fi ‘yan Afirka sanin batutuwan Afirka, kuma sun fi Sinawa sanin abubuwa da suka shafi kasar Sin. Saboda haka su kan baiwa sauran kasashe umarni kan a yi kaza da kaza, ba tare da la’akari da alhakin sakamakon da zai biyo bayan umarninsu ba. Ta wannan hanya kasashen yammacin duniya sun keta hakkin dimbin mutane na kasashe daban daban. Idan ba a manta ba, yakin da aka kai kasar Iraki ya yi sanadin rayukan dubun-dubatar jama’ar kasar, kana shirin “daidaita tsare-tsaren tattalin arziki” da suka gabatar wa kasashen Afirka, shi ma ya haifar da barna matuka.
A ganin kasar Sin, babu wata kasa da take iya tabbatar da hakkin dan Adam na dukkan bangarori a lokaci guda, saboda haka ya kamata a tabbatar da su daya bayan daya. Gwajin da kasar ta yi, ya sheda cewa, yadda aka fara da mai da hankali kan hakkin dan Adam na raya tattalin ariziki, da kawar da talauci, da zamanintar da kasa, ya haifar da nasarori. Ta hanyar raya kasa a kai a kai, kasar Sin ta cimma burinta na kawar da talauci a cikin gidanta a shekarar 2021, kana jama’ar kasar suna kan hanyar zama masu wadata, wadanda ke more ingantaccen hakkin dan Adam. Amma idan ba a bi wani daidaitaccen tsari ba, ana iya gamuwa da wahala. Misali, wasu kasashe masu tasowa sun bi umarnin kasashen yamma, inda suka siyantar da batun hakkin dan Adam, daga baya wadannan kasashe suka shiga wani yanayin da ya yi kama da na kasar Haiti, inda aka samu dimbin jam’iyyun siyasa da suke ja-in-ja da juna, da keta doka da ‘yan daba suke yi, gami da fuskantar koma bayan tattalin arziki. Yunwar da jama’ar kasar ke fama da ita, ta haifar da tarzoma a kasar, wadda ta raunana hukumomin kasar, har ma suka zama tamkar ba su da wani tasiri, matakin da ya tilasta musu dogaro kan sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD wajen tabbatar da doka da oda a kasar.
A takaice dai, harkar raya hakkin dan Adam za ta dinga samun ci gaba a duniya, idan har babu wanda ke tsoma baki ko neman yin babakere a wannan fanni. Saboda haka, kamata ya yi kasashe masu tasowa su mai da cikakken hankali kan bukatarsu ta raya tattalin arziki, yayin da suke kokarin kare hakkin dan Adam, maimakon baiwa kasashen yamma damar yin babakere a duniya kan batun kare hakkin dan Adam. (Bello Wang)