Ya kamata nahiyar Turai ta yi taka-tsan-tsan kar Amurka ta sake yi mata yankan baya
2022-03-28 20:01:26 CRI
A jiya ne agogon wurin, shugaban Amurka Biden ya koma Washington, fadar mulkin Amurkar bayan ziyarar kwanaki uku da ya kai Turai.
Idan dai ba a manta ba, a lokacin da shugaban na Amurka ya gabatar da jawabi a birnin Warsaw na kasar Poland, ya bayyana cewa Putin ba zai ci gaba da zama kan mulki ba, kalamin da ya janyo cece-kuce a tsakanin kasashen duniya.
Nahiyar Turai dai ta nuna taka tsantsan. Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya jaddada cewa, bai kamata mu bar al'amura su rincabe ba, ko dai kalamai ko a aikace.
Amurka dai ta zaku a ci gaba da yakin, ta yadda za ta samu moriya. Kana a daya bangaren, nahiyar Turai na fatan kasashen Rasha da Ukraine, za su hanzarta tsagaita bude wuta tare da maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali. A halin yanzu, Nahiyar Turai na fuskantar matsin lamba daga hauhawar farashin man fetur da iskar gas, kuma jama'a na cikin kunci.
Tilastawa nahiyar Turai ta daba wa kanta wuka, sannan su ci gaguminta, kasar da za ta iya zaluntar kawayenta ita ce Amurka! (Ibrahim)