logo

HAUSA

Jam’iyyar APC ta Nijeriya ta zabi sabon shugabanta gabanin babban zaben 2023

2022-03-28 10:23:59 CMG Hausa

Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya, ta zabi Abdullahi Adamu, sanata mai wakiltar arewa maso tsakiyar jihar Nassarawa, a matsayin sabon shugabanta, gabannin babban zaben kasar dake tafe a badi.

Abdullahi Adamu wanda ya samu gogoyn bayan shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya zama shugaban ne bayan wasu ’yan takara 6 sun janye aniyarsu ta tsayawa takara yayin babban taron jam’iyyar da aka shirya jiya Lahadi a Abuja, babban birnin kasar.

An zabi sabon shugaban ba tare da wani dan takara dake kalubalantarsa ba, bayan kuri’a ta murya da aka yi yayin taron, wanda ya samu halartar wakilai da mambobin jam’iyyar daga dukkan jihohin kasar ta yammacin Afrika, ciki har da Shugaba Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo, da shugaban majalisar dattijai da na majalisar wakilai ta kasar.

Jam’iyyar ta shafe watanni 21 ba tare da wani kwakwaran shugabanci ba, inda kwamitin riko karkashin gwamnan jihar Yobe, ya rika jan ragamarta. (Fa’iza Mustapha)