logo

HAUSA

Babban jami’in al-Shabab ya mika wuya yayin da ake sabunta shirin yakar kungiyar

2022-03-27 15:51:48 CMG Hausa

Wani babban jami’in kungiyar al-Shabab ya mika wuya ga dakarun sojojin gwamnatin Somali a ranar Asabar, a yayin da dakarun tsaron kasar ke cigaba da ayyukan murkushe mayakan kungiyar ‘yan ta’addan a shiyyar kudu maso yammacin kasar.

Jami’an rundunar sojojin gwamnatin kasar Somali (SNA), sun bayyanawa gidan radiyo mallakin kasar dake Mogadishu cewa, babban mayakin kungiyar wanda ya jima yana shirya hare hare a garin Baidoa da kewayensa, a cikin sama da shekaru biyar, ya mika wuya ga sojojin gwamnatin SNA.

A baya bayan nan, shugabannin kungiyar al-Shabab da dama sun mika wuya ga sojojin gwamnati, a yayin da dakarun tsaron ke cigaba da ayyukan murkushe mayakan a shiyyoyi kudanci da tsakiyar kasar.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da mayakan ke cigaba da kaddamar da munanan hare hare kan wakilan gwamnati da jami’an hukumar zabe dake gudanar da ayyukan shirya babban zaben kasar.

A ranar Laraba, kungiyar masu tsattsauran ra’ayin ta kaddamar da wani hari mafi muni a babban birnin kasar Mogadishu, da kuma yankin da fadar shugaban kasar take dake garin Beledweyne, lamarin da yayi sanadiyyar kashe sama da mutane 50, kana sama da mutane 100 suka jikkata a sanadiyyar harin.(Ahmad)