logo

HAUSA

Shugabannin ECOWAS sun hadu domin tattauna yanayin da Mali da Guinea da Burkina Faso suke ciki

2022-03-26 16:19:55 CMG Hausa

 

Kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afrika ECOWAS, ta gudanar da taron shugabannin kasashe da gwamnatoci mambobinta a jiya Juma’a, domin tattauna yanayin siyasar kasashen Mali da Guinea da Burkina Faso.

Shugban kugiyar, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya bayyana yayin bude taron irinsa na 5 da aka yi game da yanayin siyasar kasashen cewa, sun hadu ne domin nazarin yanayin kasashen 3 mambobin kungiyar tare da daukar matakan da suka dace na samun ci gaba.

Yayin taron manema labarai da aka yi bayan taron, shugaban hukumar kula da ECOWAS Jean-Claude Brou, ya sanar da cewa, za a ba gwamnatin rikon Mali wa’adin watanni 12 zuwa 16 a kan watanni 18 na riko da aka ba ta a baya, wanda ya kare a watan Febrerun 2022. Ya kuma bayyana cewa, takunkumin da aka sanyawa kasar za ta ci gaba da aiki idan har gwamnatin ta gaza mutunta wa’adin rikon. (Fa’iza Mustapha)