logo

HAUSA

Wasan kwaikwayo na Jingju mai tarihi da ya tsallake shingen harsuna

2022-03-25 20:05:37 CRI

 

Wasan kwaikwayon gargajiya na kasar Sin da ake kira Jingju, ko kuma Peking Opera a Turance, yana da wani tarihin da tsawonsa ya kai fiye da shekaru 200. Wanda ya kunshi fasahohin al’adu daban daban, irinsu fasahar rera waka, da samar da kide-kide, da rawa, da adabi, da dai sauransu. Zuwa wannan zamanin da muke ciki, wasan kwaikwayon ya zama wani muhimmin bangare na fasahohin al’adun gargajiyar kasar Sin, wadanda Sinawa ke matukar darajantar su.