logo

HAUSA

NATO: Da Gaske Ne Kasashen Amurka Da Turai Suna Hada Kansu?

2022-03-25 21:25:45 CMG Hausa

Ranar 24 ga wata, kungiyar tsaro na NATO ta gabatar da wani hoto mai dauke da dukkan shugabannin kasashen Amurka da Turai wadanda suka halarci taron kolin kungiyar a shafinta na intanet, lamarin da ya nuna alamar cewa, kasashen Amurka Turai suna hada kansu sosai kamar yadda suka yi a baya.

Amma da gaske ne? Hakika dai wannan kawancen aikin soja mafi girma a duniya, tana fuskantar shakkun da ake yi masa kan cewa, ko an kafa ta ne bisa doka? Sa’an nan kuma akwai sabani a tsakanin mambobin kungiyar.

Alal misali, ko da yake kasashen Amurka da Turai sun dauki ra’ayin rikau kan kasar Rasha, amma akwai bambanci a tsakaninsu. Kasashen Turai suna dogaro da makamashin Rasha. Don haka a farkon wannan wata, Amurka ta yi shelar hana sayen makamashin Rasha, amma kasashen Turai ba su bi sahunta ba. Kasashen Turai za su samu isasshen makamashi, idan har sun gaggauta warware rikicin Ukraine cikin ruwan sanyi kuma cikin hanzari. Ba shakka Amurka ta san haka. Amma ta kau da kai daga bukatun Turai. Kamar yadda tsohon dan majalissar dokokin kasar Birtaniya George Galloway ya fada, Amurka za ta bar kasashen Turai su sadaukar da kansu, kamar yadda ta shirya barin Ukraine ta saukar da kanta.

Da gaske ne irin wannan Amurka ta cancanci kawayenta na yammacin duniya su gaskata ta? (Tasallah Yuan)