logo

HAUSA

Ashe, akwai bambanci a tsakanin 'yan gudun hijira?

2022-03-25 14:00:50 CRI

Tun bayan barkewar yaki tsakanin Rasha da Ukraine, adadi mai yawa na ‘yan gudun hijirar Ukraine ne suka yi ta kwarara wasu kasashen yammacin duniya. Idan aka kwatanta da ko in kula da suka nuna, tare da rufe kofofinsu ga ‘yan gudun hijirar yankin gabas ta tsakiya da Afrika da sauran wasu yankuna a shekarun baya-bayan nan, kasashen yammacin duniya sun tausayawa ‘yan gudun hijirar na Ukraine. Wasu ‘yan siyasa da kafofin watsa labarai na kasashen yamma, su na amfani da launin fata a matsayin wata ka’ida ta kwatanta ‘yan gudun hijirar Ukraine, da na yankin gabas ta tsakiya da Afrika, inda suke bayar da fifiko ga ‘yan Ukraine din.

Misali, Firaministan Bulgaria Kiril Petkov, ya ce: “wadannan ‘yan gudun hijirar na Ukraine, sun bambanta da mutanen da muka gani a baya. Dukkansu Turawa ne, wadanda su ka yi karatu. A baya kuwa, akwai yuwuwar wasu daga cikinsu ‘yan ta’adda ne”. Dan jaridar kafar CBS a Kiev Charlie D'Agata, a rahotonsa ya ce, “wannan ba wuri ne da aka shafe gomman shekaru ana ta rikice-rikice kamar Iraqi ko Afghanistan ba, wannan wuri ne mai wayewar kai, kuma a Turai”.

Wadannan kalamai sun bayyana irin zurfin wariyar launin fata da fadin rai da suka yi wa Amurka da sauran kasashen yamma katutu. Kalamai da abubuwan da suka yi na nuna fuska biyu game da batun ‘yan gudun hijira da ayyukan jin kai, sun kara nuna irin munafurcinsu na rajin kare hakkin bil adama.(Mai zane: Mustapha Bulama)