logo

HAUSA

Masaniya ta bukaci a kara zuba jari wajen yaki da cutar tarin fuka a Afrika

2022-03-25 11:28:24 CMG Hausa

Wata masaniya kan cutar Tarin Fuka a Afrika, Lucica Ditiu, ta ce ba za a cimma burin da ake da shi na fattakar cutar Tarin Fuka daga nahiyar Afrika ba, har sai an kara zuba isasshen jari ga ayyukan kandagarki da duba masu cutar da kuma jinyarsu.  

Lucica Ditiu, wadda ita ce babbar daraktar shirin kawance na Stop TP, wata cibiyar kasa da kasa mai yaki da cutar Tarin Fuka, ta ce dole ne kasashen Afrika da abokan huldarsu su shawo kan matsalar kudi da ake fuskanta domin farfado da yaki da cutar mai yaduwa.

Wata sanarwar da Lucica Ditiu ta fitar a Nairobin Kenya, domin ranar yaki da cutar Tarin Fuka ta duniya, ta ruwaito cewa, ana fama da karancin kudin yaki da cutar a Afrika idan aka yi la’akari da yadda cutar ta yi kamari har ma take iya kai wa ga asarar rai. (Fa’iza Mustapha)