Ya Zuwa Yanzu Amurka Tana Rura Wuta Tsakanin Rasha Da Ukraine
2022-03-24 21:10:18 CMG Hausa
Ranar 14 ga wata, an cika wata guda da fara yin musayar wuta a tsakanin kasashen Rasha da Ukraine. Shugaban kasar Afirka ta Kudu Matamela Cyril Ramaphosa, da sauran al’ummun kasa da kasa suna ganin cewa, ainihin dalilin da ya sa ake zaman dar dar a tsakanin Rasha da Ukraine shi ne shigar da kasashe tsoffin mambobin Soviet, da kasashen tsakiya da gabashin Turai cikin kungiyar tsaro ta NATO a shekaru da dama da suka wuce. Kasashen yammacin duniya, musamman ma kasar Amurka sun dauki alhakin yakin.
Duk da suka da aka sha yi, amma Amurka tana kara rura wutar yakin, a yunkurin ganin Rasha da Ukraine sun ci gaba da yaki a tsakaninsu.
Kwanan baya, shugaba Joe Biden na Amurka ya fara ziyara a kasashen Turai. Amurka ta yi shelar cewa, a yayin ziyararsa, za a tabbatar da sabbin matakai kan Rasha, ciki har da sabbin matakan sanya wa Rasha takunkumi. Yanzu an cika wata guda da yin musayar wuta a tsakanin Rasha da Ukraine. Idan Amurka ta hada hannu da kawayenta na yammacin duniya, wajen tsananta takunkuman da za su sanya wa Rasha, to, za a kara rura wutar yakin, kuma kowa zai fahimci makarkashiyar Amurka ta haifar da tashin hankali a duniya.
Abin da ya kamata a lura da shi shi ne, Jake Sullivan, mai ba da taimako ga shugaban Amurka kan harkokin tsaron kasa, ya ambato ziyarar Biden a Turai da cewa, rikicin da ke tsakanin Rasha da Ukraine ba zai kawo karshe cikin hanzari ba. Lallai wannan shi ne manufar da Amurka ke neman cimmawa. Tana ingiza ci gaba da yin yaki a tsakanin Rasha da Ukraine, a yunkurin muzgunawa Rasha, da dakile Turai, da kawo wa rukunonin masana’antun aikin soja riba, da inganta yin danniya a duniya. (Tasallah Yuan)