Dabarun Kimiyya Da Nacewa Bin Ka’idoji Ne Jigon Shawo Kan Annobar COVID-19 A Sin
2022-03-24 19:03:51 CRI
Masana kiwon lafiya na hasashen cewa, kasar Sin za ta ci gaba da wanzar da nasarorin da take samu, a yakin da take yi da annobar COVID-19, duk da sake bullar cutar da ake samu a wasu sassan kasar a baya bayan nan.
Tun bullar wannan annoba a kasar yau shekaru 2 da suka gabata, mahukuntan kasar sun aiwatar da matakai daki daki na dakushe bazuwar ta, wadanda suka yi matukar tasiri wajen dakushe kaifin ta. Babban sirrin nasarar da kasar ta cimma ya zuwa yanzu dai shi ne nacewa bin dabarun kimiyya, da bin ka’idojin masana, ta yadda kasar ta kai ga cimma daidaito tsakanin matakan yaki da annobar, da kuma bunkasar ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma.
Wasu daga masu fashin baki, game da yanayin bazuwar annobar COVID-19 na ganin cewa, abu ne mai wahala cutar ta bace baki daya cikin kankanen lokaci, musamman idan aka yi la’akari da yanayin bullar sabbin nau’o’inta a sassan duniya daban daban. Don haka dabarun kimiyya da Sin ta aiwatar tun da fari, kama daga matakan kandagarki zuwa na rigakafi, da ka’idojin ba da tazara, da taimakawa sauran sassan kasashen duniya da kayan yaki da annobar, da alluran rigakafi, sun yi matukar tasiri wajen rage kaifin bazuwar cutar a cikin gida, da ma sauran sassan duniya.
Kamar yadda Sinawa kan ce "Nasara na samuwa ne bayan juriya", kasar Sin ba ta yi kasa a gwiwa ba, wajen daukar dukkanin matakai da suka wajaba, ta kuma rungumi manufar tabbatar da yakar cutar baki daya. Karkashin wannan manufa, kawo yanzu, ana ci gaba da gudanar da gwajin cutar, da bin diddigin wadanda suka yi cudanya da masu dauke da ita, tare da sanya ido matuka wajen jagorancin dukkanin ayyukan yaki da cutar.
Ko shakka babu, irin wadannan matakai da tuni suka yi tasiri a nan kasar Sin, kamata ya yi su zamo abun misali ga sauran sassan duniya, dake fuskantar yaduwar wannan annoba, wadda kawo yanzu ta yi mummunar barna, ga yanayin tattalin arziki da zamantakewar al’ummun duniya baki daya. (Saminu Hassan)