logo

HAUSA

Rundunar sojojin Najeriya ta ce kimanin ‘yan ta’adda dubu 7 sun mika wuya a mako guda

2022-03-24 11:16:00 CMG Hausa

Wani babban jami’in rundunar sojojin Najeriya ya bayyana a ranar Laraba cewa, kimanin mayaka masu tsattsauran ra’ayi 7,000, da suka hada da mayakan Boko Haram, da na kungiyar masu da’awar kafa daular musulunci a yammacin Afrika (ISWAP), sun mika wuya ga sojojin Najeriya a makon da ya gabata.

Yakin da sojojin Najeriya ke yi da mayakan ISWAP da na Boko Haram, yana ci gaba da samun gagarumar nasara, kamar yadda Christopher Musa, kwamandan dake jagorantar yakin da sojojin Najeriya ke yi a jihar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Ana sa ran wadanda suka mika wuya tare da iyalansu, za su kasance karkashin kulawar sojojin Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki gabanin shirya horon sauya tunaninsu.

Jami’in ya ce, sojoji da sauran hukumomin tsaro, za su ci gaba da aiwatar da kyawawan dabarun kawo karshen ayyukan ta’addanci a shiyyar. (Ahmad)