logo

HAUSA

Kura Ce Za Ta Cewa Kare Maye

2022-03-23 21:43:30 CMG Hausa

Kwanan baya, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ya yi shelar cewa, za a sanya kaidi kan bisar jami’an kasar Sin, bisa hujjar hakkin dan Adam. Lallai ‘yan siyasan Amurka da suka keta hakkin dan Adam sun mayar da fari baki. Kura ce za ta cewa kare maye. Sun nuna fuska biyu, da rashin sahihanci kan hakkin dan Adam. Wadannan masu rajin kare hakkokin bil Adama sun yi danniya ne da sunan kare hakkin dan Adam.

Rana guda kafin Blinken ya sanar da hakan, wato ranar 20 ga watan Maris, an cika shekaru 19 da barkewar yakin kasar Iraki. Ya zuwa yanzu, Amurka ba ta nuna wa duniya wasu shaidu don gane da dalilin da ya sa ta tayar da yakin, wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula kusan dubu 200 ba. Abubuwan da suka faru a kasashen Iraki, Afghanistan, Syria, da Ukraine sun nuna cewa, Amurka, kasa ce wadda ta fi ko wace keta hakkin dan Adam a duniya.

A sa’i daya kuma, wajibi ne ‘yan siyasar Amurka su yi bayani, kan dalilin da ya sa ita dake matsayin mafi karfin ci gaba a duniya ta fi gazawa wajen yaki da annobar COVID-19! Yanzu miliyoyin Amurkawa sun mutu sakamakon annobar.

Jama’ar Sin suna da ikon fada a ji a fannin kiyaye hakkin dan Adam a kasarsu. Har kullum jam’iyyar da ke mulkin kasar tana mayar da jama’arta a gaban komai, a fannonin kiyaye lafiyar al’ummarta, da fitar da dukkan jama’a daga kangin talauci da dai sauransu. Rahoton bincike na kasa da kasa na shekarar 2020, wanda kamfanin binciken ra’ayoyin jama’a na Ipsos na kasar Faransa ya gabatar ya nuna cewa, kasar Sin, kasa ce wadda jama’arta suka fi jin dadin zama. Jama’ar Sin da yawansu ya kai kaso 93 cikin dari suna ji dadin zamansu sosai. Wanna shi ne abun da ke shaida nasarar kasar Sin ta fannin kiyaye hakkin dan Adam. (Tasallah Yuan)