Sin da kasashen Afirka na da matsaya guda game da inganta hadin gwiwa
2022-03-23 09:59:55 CMG Hausa
A kwanan nan babban dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya gana da ministan harkokin wajen kasashen Zambiya, da Algeriya, da Tanzania.
Yayin tattaunawar jami’an, Wang Yi ya kara jaddada matsayar kasar Sin, game da fatanta na ci gaba da hadin gwiwa da sassan nahiyar Afirka, a fannonin yaki da cutar COVID-19, da kiwon lafiya, da raya shawarar “ziri daya da hanya daya”, da taimakawa bunkasa nahiyar Afirka, da sa kaimi ga raya tsarin demokuradiyya, a fannin dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, da kara yin mu’amala kan harkokin kasa da kasa, ta yadda za su kara sada zumunta da juna, da zurfafa hadin gwiwarsu baki daya.
Wata muhimmiyar gaba ta tattaunawar jami’an ita ce batun rikicin Ukraine, wanda ministocin harkokin wajen Sin din ya bayyana a matsayin tashin hankali da ya yi babban tasiri ga yanayin nahiyar Turai, da ma sauran sassan duniya baki daya. Wang Yi na ganin duniya tana kunshe da kasashe da dama, ciki har da wasu dake kara rura wutar tashin hankali, amma Sin da kawayenta na nahiyar Afirka, na fatan za a koma teburin shawara, tare da kaucewa daukar bangare a rikicin dake wakana.
A nasu bangare, ministocin harkokin wajen Zambiya, da Algeriya, da Tanzania, bi da bi, sun jinjinawa matsayar Sin na kaucewa kara rura wutar tashin hankali, da irin kiraye kiraye da take yi na ganin an kai zuciya nesa, da komawa teburin sulhu ba tare da bata lokaci ba.
Ko shakka babu a matsayinsu na kasashe masu tasowa, Sin da kasashen Afirka sun lura da muhimmancin zaman lafiya, a wannan gaba da ake fuskantar kalubalen tashin hankali tsakanin Rasha da Ukraine, musamman ganin yadda hakan ya haifar da tashin farashin makamashi da albakarun gona, da kwararar ’yan gudun hijira, lamarin da muddin ba a gaggauta kawo karshensa ba, na iya haifar da kara tabarbarewar tattalin arziki, da yanayin zamantakewar al’ummun sassan duniya da dama.