logo

HAUSA

Najeriya na da burin cimma kashi 95 na cimma Ilimin zamani nan da 2030

2022-03-23 11:14:54 CMG Hausa

Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani na Najeriya, Isah Pantami ya bayyana cewa, gwamnatin Najeriya ta kudiri aniyar cimma kashi 95 cikin 100 na ilimin zamani nan da shekarar 2030.

Da yake jawabi a yayin wani taron masu ruwa da tsaki a Abuja, babban birnin kasar, ministan ya ce, ’yan kasar za su iya ba da gudummawa ga raya tattalin arzikin kasar ta hanyar yin kirkire-kirkire da bullo da hanyoyin magance matsalar da ’yan kasar ke fuskanta.

Pantami ya ce, bayanai na zamani wani fanni ne mai fadin gaske, wanda tuni yake sauya kowane salon rayuwa. A don haka ya yi kira ga 'yan Najeriya, da su samar da shawarwarin da za su hanzarta samun nasarar da ake fatan cimmawa, na mayar da kasar bisa takarfi na zamani. (Ibrahim)