logo

HAUSA

Kwarewar Sin Ta Raya Tattalin Arziki Ta Amfani Duniya Baki Daya

2022-03-23 19:06:37 CRI

Sanin kowa ne cewa, har yanzu duniya na fama da tasirin annobar COVID-19, matakin da ya kara cusa tattalin arziki da sauran fannoni na rayuwar yanayi na rashin tabbas. Sai dai duk da wannan kalubale, hukumomin kudi irinsu IMF, da babban bankin duniya, sun bayyana cewa, kasar Sin ce kasa daya tilo a duniya da tattalin arzikinta zai kai wani mataki mai kyau na samun bunkasa, biyo bayan matakan da kasar ta dauka wajen yaki da wannan annoba.  A kwanakin baya, shugaban dake kula da harkokin yankunan da Sinawa suke zaune na bankin OCBC na kasar Singapore Tommy Xie, ya bayyana cewa, kasar Sin tana da kwarewa wajen raya tattalin arziki, sabo da managartan manufofi da gwamnatin kasar ta tsara, gami da sauran dalilai.

Masharhanta na cewa, irin wadannan manufofin da kasar Sin ta tsara, sun taimakawa kasar wajen fuskantar kalubaloli, kamar karancin kayayyakin da ake shigowa da su. Kuma tun gabanin karuwar farashin makamashi da manyan hajoji a kasashen duniya, gwamnatin kasar Sin ta tsara matakai da dama domin daidaita matsalar, lamarin da ya nuna kwarewarta wajen kare yanayin ci gaban tattalin arzikin kasar. Matakin da zai taimaka wajen ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya.

Yayin da bukatun al’umma kan sabbin makamashi ke kara karuwa sakamakon tashin farashin makamashi da hauhawar farashin a kasashen duniya, a hannu guda kuma, sabbin makamashi na kara tasiri kan bunkasuwar tattalin arzikin kasar, su ma kamfanonin da abin ya shafa, za su ci gaba da samun bunkasuwa yadda ya kamata a kasar Sin.

Idan ba a manta ba, yayin zama na biyar na taron wakilan jama’ar kasar Sin karo na 13, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta taka rawar gani a dukkan fannoni duk da kalubalen da duniya ta tsinci kanta a cikin sanadiyar annobar COVID-19. Gwamnatin kasar Sin ta mayar da hankali wajen tabbatar da kyautata rayuwar jama'a da nufin bunkasa tattalin arziki, da kara mayar da hankali wajen neman gaskiya da shaidu na zahiri da sauraron muryoyi da bukatun jama’a. Wannan a cewar masu fashin baki, kwarewa ce mai ma’ana.

Duk mai bibbiyar al’amura ya fahimci cewa, irin matakai da manufofin da kasar Sin ta dauka, tun lokacin da ta bude kofarta ga kasashen waje fiye da shekaru 4, sun taimaka mata wajen samun ci gaban kanta, da amfanar da jama’a da ma duniya baki daya. Mahukuntan kasar dai sun sha nanata cewa, wannan wata muhimmiyar dama ce da kasar ba za ta taba rufewa ba, kuma tilas ba za ta rufe ba. Ai da ma sai an zubar da ruwa a kasa kafin a taka damshi. (Ibrahim Yaya)