logo

HAUSA

"Daular Karya" Na shan Barasha Don Murnar Rikicin Dake Tsakanin Rasha Da Ukraine

2022-03-23 10:26:45 CRI

"Tun lokacin da rikici ya barke tsakanin Rasha da Ukraine, a cikin ma'aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon, da K Street (wurin tarukan kamfanoni masu janyo ra’ayi a Washington), masana'antun samar da kayayyakin soja, da kuma cikin ginin Capitol, ana can ana ta shan barasha don murna!" Franklin C. Spinney, kamar yadda tsohon jami'in ma'aikatar tsaron Amurka ya yi tsokaci a baya-bayan nan, hakan ya nuna cewa, Amurka ce ta fi kowa cin moriyar rikicin dake faruwa a tsakanin Rasha da Ukraine.

Kamar yadda Spinney ya yi nazari, rikici tsakanin Rasha da Ukraine ya barke ne sakamakon magudin siyasa. Amurka, wacce ta fara tayar da rikicin Ukraine, ba wai kawai ta sanya masana’antunta na samar da kayayyakin soji suna samun makudan kudade ba, har ma ta danne Rasha ta hanyar kara sanya mata takunkumai, kana ta dakile yunkurin Turai na neman 'yancin kai, da kuma karfafa matsayinta na nuna danniya ko babakere.

Duniya ta gani a fili cewa, "Daular Karya", wato kasar Amurka dake karfafa tsanantar rikici, da amfani da rikicin don samun moriya, take kuma kwankwadar barasa don murnar, ita ce ta haddasa rikicin Ukraine. Mai fassara: Bilkisu Xin)