logo

HAUSA

’Yan bindiga sun kashe mutane 34 a arewacin Najeriya

2022-03-23 10:17:51 CMG Hausa

Rahotanni daga Najeriya sun tabbatar da cewa, a kalla mutane 34 ne aka kashe, biyo bayan wasu hare-haren da wasu ’yan bindiga suka kai a wasu kauyuka hudu a jihar Kaduna, dake yankin arewa maso yammacin Najeriya a ranar Lahadi.

Kwamishinan tsaro na harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan, ya shaidawa taron manema labarai a birnin Kaduna, babban birnin jihar cewa, mutane 7 ne suka jikkata, yayin da aka kona gidaje sama da 200 da shaguna 32 a hare-haren da aka kai a daren ranar Lahadi a kauyukan Tsonje, da Agban, da Katanga, da Kadarko dake karamar hukumar kaura.

Kawo yanzu dai, babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin. (Ibrahim)