logo

HAUSA

Samaila Umaru: Allah ya kara dankon zumunci tsakanin Afirka da Sin

2022-03-22 14:27:14 CRI

Samaila Umaru, ma’aikaci ne daga jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya a Najeriya, wanda yake matsayin aro a jami’ar sojojin sama wato air force institute of technology a halin yanzu a matsayin farfesa. Ya taba yin karatun neman digiri na uku har tsawon shekaru biyar a kasar Sin, musamman a birnin Changsha dake lardin Hunan.

A yayin zantawarsa da Murtala Zhang, malam Samaila Umaru ya bayyana ra’ayinsa kan bambancin yanayin karatu tsakanin gida Najeriya da kasar Sin, da yadda ya fahimci al’adun kasar.

Malam Samaila Umaru ya ce, kishin kasa na daya daga cikin muhimman dalilan da suka jawo ci gaban kasar Sin, don haka, ya yi kira ga daliban Najeriya da ma Afirka dake kasar Sin, su kara kokari don ganin sun samu ilimi mai amfani. (Murtala Zhang)