logo

HAUSA

Hadin Gwiwar Kasar Sin Da Kungiyar Kasashen Musulmi Zai Kawar Da Jita-jitar Da Ake Yadawa Game Da Kasar

2022-03-22 19:39:17 CRI

Majalisar ministocin harkokin wajen kungiyar kasashe musulmi OIC, na gudanar da taronta karo na 48 daga yau Talata, zuwa gobe Laraba, inda a karon farko ya samu halartar mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi.

Ko ba a fada ba, wannan wani gagarumin mataki ne da zai tabbatar da zaman lafiya da kore duk wata jita-jitar da kafafen yada labaran kasashen yammacin duniya ke yadawa da zummar shafawa Sin bakin fenti.

Karbar bakuncin ministan harkokin wajen kasar Sin da kungiyar ta yi, babbar alama ce dake cewa, suna goyon bayan ayyukan da kasar Sin ke yi na yaki da ta’addanci, haka kuma sun san hakikanin yanayin da yankin kasar Sin dake da rinjayen musulmi ke ciki.

Kamar yadda Wang Yi ya fada, wannan wani muhimmin bangare ne na huldar kasashe masu tasowa. A matsayin kasar Sin na babbar kasa mai tasowa cikin sauri a duniya, da kasashen kungiyar OIC na kasashe masu tasowa, hadin gwiwa a tsakaninsu abu ne mai matukar amfani, domin za su amfana da irin manufofi da dabarun kasar Sin na ci gaba. Haka kuma, za su ci gajiyar irin taimakonta mara sharadi, sannan za su gudanar da hadin gwiwar mai tsafta bisa adalci da girmama juna ba tare da katsalandan cikin harkokinsu na gida ba.

A cewar Wang Yi, kasar Sin da kasashen musulmi, na da buri mai karfi na hadin gwiwa domin tabbatar da hadin kai da adalci da samun ci gaba, wadanda abubuwa ne da ake bukata a wannan lokaci da duniya ke fuskantar kalubale mabanbanta kana wasu kasashe ke kokarin rura wutar rikici da kawo rarrabuwar kawuna tsakanin al’ummomi.