logo

HAUSA

Taron kolin ruwa na duniya karo na 9 ya mayar da hankali kan samar da ruwa don zaman lafiya da ci gaba

2022-03-22 10:43:01 CMG Hausa

A ranar Litinin, an bude taron kolin samar da ruwa na kasa da kasa karo na 9, a Dakar, babban birnin kasar Senegal, mai taken, “Samar da ruwa domin zaman lafiya da ci gaba.”

Taron na kwanaki shida, shi ne irinsa na farko da ake gudanarwa a wata kasa daga yankin hamadar Afrika. Taron kolin zai kunshi wasu jerin taruka da za a gudanar, wadanda za su ba da fifiko kan fannoni hudu: da suka hada da samar da ruwa da tsaftar muhalli, da samar da ruwa don bunkasa karkara, da hadin gwiwa, da kuma amfani da ruwa a matsayin kayan aiki kuma jigon rayuwa.

Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya jagoranci bude taron, wanda ya samu halartar shugabannin kasashen Afrika da dama.

Jami’ai daga hukumomin kasa da kasa, da masu tsara dabarun ci gaba, da masana daga jami’o’i na daga cikin mahalarta taron kolin. (Ahmad)