logo

HAUSA

Bai Kamata A Bar Kasashen Afirka Su Zama Filin Ciyayin Da Manyan Giwaye Ke Fada A Kai Ba

2022-03-21 20:37:42 CRI


Sharhi daga Bello Wang

Jiya Lahadi, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan wajen kasar, Wang Yi, ya gana da takwarorinsa na wasu kasashen Afirka, da suka hada da Aljeriya, da Zambia, inda suka tattauna maganar Ukraine. Yayin tattaunawar, ministan wajen kasar Aljeriya, Ramtane Lamamra, ya ce, yanzu haka ana keta hakkin kasashe masu tasowa, ta hanyar tilasta musu daukar wani bangare, har ma da yin watsi da ‘yancinsu na tsara manufofin diplomasiyya. Maganarsa ta nuna abun dake ciki zukatan dumbin kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen dake nahiyar Afirka: Yadda kasar Amurka da kawayenta suke tilastawa sauran kasashe saka takunkumi kan kasar Rasha, bai dace ba.

Bayan barkewar wutar yaki tsakanin Rasha da Ukraine, kasar Amurka da wasu kawayenta suna fakewa da kalmar “adalci”, suna kokarin matsawa kasashe masu tasowa lamba, don neman sanya su cikin kasashen da suka kakaba wa kasar Rasha takunkumi. Sai dai, tambayar ita ce, shin kasar Amurka da kawayenta za su iya wakiltar “adalci”? Dangane da batun, shugaban kasar Afirka ta Kudu, Matamela Cyril Ramaphosa, ya tona asirin kasar Amurka a kwanan baya, inda ya ce, dalilin da ya sa aka samu barkewar yaki a Ukraine, shi ne yadda kungiyar NATO dake karkashin jagorancin kasar Amurka, ke kara habaka karfin ta zuwa gabas cikin shekarun nan. A nan kasar Amurka ta yi wayo, inda ta ta da rikici da farko, sa’an nan ta saka wa kasar Rasha takunkumi, wadanda dukkansu matakai ne na dakushe Rasha din.

Ta hanyar saka wa Rasha takunkumi, kasar Amurka za ta iya tabbatar da karfinta na yin babakere a duniya, sai dai kuma me wannan mataki zai haifar ga kasashe masu tasowa? Mun san kasar Rasha tana cikin kasashen da suke fitar da dimbin amfanin gona zuwa ketare. A shekarar 2020, darajar amfanin gona da kasashen Afirka suka shigar da su daga Rasha ta kai dalar Amurka bilian 4. Kana kasashen Masar, da Sudan, da Najeriya su ne wadanda suka shigo da mafi yawan amfanin gona daga Rasha. Saboda haka, yadda ake sanya wa Rasha takunkumi zai rage karfin wadannan kasashen na samar da isashen abinci ga jama’arsu.

Ban da wannan kuma, kasar Rasha na samar da danyen mai da iskar gas da yawansu ya wuce kashi 10% cikin daukacin mai da gas da ake samar da su a duniya. Saboda haka, idan an hana ta fitar da mai da gas, hakan zai yi mummunan tasiri kan kasuwannin duniya. Wasu sun ce, hauhawar farashin mai tana da kyau ga kasar Najeriya mai samar da mai. Sai dai jama’ar kasar Najeriya ba za su yarda da maganar ba, domin har yanzu suna jin radadin matsalar karancin mai a kasuwannin kasar, lamarin da hauhawar farashin mai ta haddasa.

Bugu da kari kuma, saka wa kasar Rasha takunkumi zai haifar da tasiri kan tsare-tsaren samar da kayayyaki na duniya, da kasuwar hada-hadar kudi ta duniya, lamarin da zai tsananta matsalar da kasashen Afirka suke fuskanta a fannin tattalin arziki, sakamakon annobar COVID-19. Wato, ja-in-ja da ake yi tsakanin Amurka da Rasha, zai sa jama’ar kasashen Afirka shan wahala, wanda kuma hakan sam bai dace ba.

Bayan da ministan wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da takwarorinsa na wasu kasashen Afirka a wannan karo, ya ce, kasar Sin da sauran kasashe masu tasowa sun riga sun cimma matsaya, dangane da hanyar da za a bi wajen daidaita batun Ukraine, wanda ya kasance: A yi kokarin kawo karshen yaki ta hanyar yin shawarwari cikin sauri, maimakon daukar matakin sanya takunkumi, wanda zai iya bata damar samun farfadowar tattalin arzikin duniya. Kana bai kamata a tilastawa wani daukar wani bangare ba, domin lamarin zai zama keta ikon mulkin kai na sauran kasashe.

Sinawa su kan ce, “ Idan giwaye sun yi fada, filin ciyayi zai sha wahala.” Yanzu haka, maganar Ukraine na haifar da tasiri a bangarorin siyasa, da tattalin arziki ga wurare daban daban na duniya, kana kasashe masu tasowa sun fi jin radadin rikicin. Har ila yau, komai yanayin da za a shiga ciki, akwai bukatar tunawa da maganar Wang Yi: Kar a manta da nahiyar Afirka, ko kuma a sake kebe ta cikin wani bangare, ba tare da lura da ita ba. Sa’an nan, kar a sa kasashen Afirka yin hasara sakamakon batun Ukraine din. (Bello Wang)