logo

HAUSA

Me Ya Haifar Da Bunkasar Cinikayyar Sin Da Afrika Duk Da Barkewar Annoba?

2022-03-21 20:29:53 CRI

Duba da irin girma da tasirin yanayin mu’amalar cudanyar juna dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, zamu iya cewa, alakarsu tana haifarwa bangarorin biyu kyakkyawan sakamako. Har kullum, bangarorin biyu na ci gaba da nuna aniyarsu da sha’awarsu na cigaba da yin mu’amala domin kyautata mokomar alummun dukka bangarorin biyu. Duk da irin mummunan tasirin da annobar COVID-19 ta haifarwa duniya ta fuskoki da dama musamman wajen karya lagon tattalin arzikin kasashen duniya, amma alakar kasuwanci dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika tana samun tagomashi. Kamar yadda wani rahoton da kamfanin bincike da bada shawarwarin kasuwanci na Global research and advisory company dake birnin Oxford na kasar Birtaniya ya fitar kwanan nan, inda ya bayyana cewa, duk da irin kalubalolin da duniya ke fuskanta a tsarin hada-hadar kasuwanci, amma cinikayya tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ta samu gagarumar bunkasuwa a shekarar 2021. Koda yake, har kullum kasar tana yawan nanata kudirinta na tallafawa kasashe masu tasowa da kuma kulla dangantaka mai karfi tsakaninta da kasashen masu tasowar ciki har da kasashen Afrika, lamarin ya sanya kasar Sin daukar wasu jerin matakai domin kyautata cudanyar kasuwanci tsakaninta da ksashen Afrika. Alal misali, a baya bayan nan, sakamakon sassauta dokokin kasuwanci da hukumar kwastom ta kasar Sin ta yiwa wasu kasashen Afrika, matakin ya bayar da damar samun karuwar kayan amfanin gona daga nahiyar Afrika zuwa kasuwannin kasar Sin, kamar yadda rahoton jaridar turanci ta South China Morning Post, dake da babban ofishinta a Hong Kong ta wallafa. A baya bayan nan, kasashen Afrika ta kudu, da Kenya da Zimbabwe, suna daga cikin kasashen da suka sanya hannu kan dokokin da aka yiwa gyaran fuska, lamarin da ya bada dama ga kasashen wajen samun shiga kasuwannin hada-hada na kasar Sin. A watan jiya, kasar Afrika ta kudu ta shigar da kashin farko na lemon tsaminta 100,000 zuwa kasar Sin. Kasar Tanzania ma ta fara shigar da waken soyarta zuwa kasar Sin a shekarar 2020. Bugu da kari, an cimma makamanciyar wannan yarjejeniyar don shigar da avocados, da ganyen shayi, da kofi da furanni daga kasar Kenya zuwa kasuwannin Sin, sai kuma gahawa da waken soya daga kasashen Habasha da Rwanda, da naman shanu daga kasashen Namibia da Botswana, da kayan lambu daga kasar Afrika ta kudu. Dukka wadannan sun taimaka wajen kara karfafa cudanyar kasuwanci tsakanin Sin da kasashen Afrika. Har kullum bangarorin biyu suna kara lalibo sabbin hanyoyin karfafa huldarsu daga dukkan fannoni domin baiwa marada kunya.(Ahmad Fagam)