logo

HAUSA

MDD ta kaddamar da aikin tallafawa ’yan gudun hijirar Somalia

2022-03-21 14:28:21 CMG Hausa

MDD da abokan huldarta sun kaddamar da wani shiri na shekaru hudu domin samar da ingantacciyar hanyar warware matsalolin da mutanen da rikici da sauyin yanayi suka tilasta musu kauracewa muhallansu a kasar Somalia.

Shirin na miliyoyin kudade wanda aka yiwa taken "Saameynta a Somaliya" zai lalibo dawwamammun hanyoyin warware matsalolin da mutane 75,000 dake rayuwa a sansanoni da alummun yankunan dake karbar bakuncin yan gudun hijirar Somalia, kamar yadda shirin hadin gwiwar na MDD ya bayyana cikin wata sanarwar da aka fitar a babban birnin Somalia.

Adam Abdelmoula, jami’in shirin jinkai na MDD a Somaliya, ya ce, samar da dawwamammun hanyoyin kawo karshen matsalolin da mutanen da suka kauracewa gidajensu ke fuskanta a Somalia, akwai bukatar inganta rayuwar mutanen dake rayuwa a sansanonin da alummun dake karbar bakuncinsu.

Abdelmoula ya ce, babu tabbacin mazauna sansanonin na IDPs za su iya komawa gidajensu na asali a nan gaba, kasancewar a halin yanzu yankunan ba su da ingantattun gonakin noma.

Karkashin shirin agajin, MDD da abokan hularta za su yi aiki tare da gwamnati domin aiwatar da shirin warware matsaloli na kasar.

A cewar MDD, shirin yana da burin lalibo hanyoyin rage dogaro kan tallafin jin kai, da rage talauci ga dubban mutanen dake fama da talauci, da kuma inganta muhallan zaman a IDPs dake biranen kasar.

Abdelmoula ya ce, tallafin jin kai kadai ba zai iya magance manyan matsaloli kamar na dubban mutanen da suka kauracewa gidajensu, da karuwar matsalar fari, da ambaliyar ruwa ba. Shi ya sa MDD ta fi ba da fifiko wajen lalibo hanyoyin warware matsalolin. (Ahmad Fagam)