logo

HAUSA

Kungiyoyin ’yan asalin kasa sun yi maraba da hukuncin kotu kan shara’ar gina helkwatar kamfanin Amazon a Afrika ta kudu

2022-03-21 11:15:31 CMG Hausa


Kungiyoyin cikin gida da na yan asalin kasa na Khoisan sun yi maraba da hukuncin da kotu ta zartar game da batun aikin gini wanda ya shafi gina helkwatar katafaren kamfanin Amazon na kasar Amurka a birnin Cape Town, helkwatar majalisar dokokin kasar Afrika ta kudu.

Kungiyar sanya ido ta alummar fararen hula wacce ke wakiltar kungiyoyin mazauna kasar da majalisar gargajiya ta yan asalin kasar, wato Goringhaicona Khoi Khoin, kungiyar ta Khoisan, ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, za su bukaci kotu ta soke izinin gudanar da aikin a yankin dake karkashin kulawarta.

Aikin na kudin kasar Rand biliyan 4, kwatankwacin dala miliyan 270, wanda aka yiwa lakabin River Club, zai shafi samar da cibiyoyin kasuwanci da ofisoshi wanda ya kai girman sikwaya mita 150,000.

Sannan kuma, kungiyar sanya idon ta Goringhaicona Khoi Khoin Indigenous Traditional Council, wato hadakar kungiyar Khoisan, ta mika bukatar gaggawa ga kotun game da aikin tana ikirarin cewa, aikin zai lalata kimar yankin wacce aka gada tun kaka da kakanni, kuma aikin ya ci karo da manufofin inganta muhalli na kasar. (Ahmad Fagam)