logo

HAUSA

Ranar barci ta duniya: bari mu yi barci da kyau

2022-03-20 17:25:55 CRI

 

Ranar 21 ga watan Maris na ko wace shekara, rana ce ta barci ta kasa kasa. Kwamitin nazarin harkokin barci na kasar Sin ya gudanar da wani bincike, inda aka gano cewa, yawan baligai masu fama da matsalar karancin barci ya kai kaso 38.2 cikin dari a nan kasar Sin, kana mutane fiye da miliyan 300 suna fama da matsalar barci a duk fadin kasar. Masu karatu, ko kun taba fama da matsalar barci?

Akwai dalilai da dama da suke haifar da matsalar karancin barci. Amma kwanciya a makare da dare ya kan illata lafiyar mutane. Idan mun ayyana ran dan Adam a matsayin gudu mai dogon zango, to, yin barci yana samar da kuzari ba tare da tsayawa ba.

Madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta ba da shawarar cewa, idan kananan yara sun yi aikin gida da yawa sun yi barci a makare a dare, to, ku gaya musu cewa, wajibi ne kullum su yi aiki tukuru, su kyautata yin karatu, a maimakon yin barci a makare da dare. Idan kun samu ayyuka da yawa, to, ku tunatar da kanku cewa, kada ku yi aiki ba dare ba rana, idan ba ku yi barci da kyau da dare ba, to, ba za ku yi aiki da kyau da rana ba. Idan wasu sun yi wasan internet ko kallon shirye-shiryen telibijin har suka yi barci a makare da dare, to, ku gaya musu cewa, ya kamata su ajiye wayarsu ko kwamfyuta, su daina hanyoyin zaman rayuwa marasa dacewa, don haka za su kyautata kansu. Haka kuma, idan wasu sun dade suna fama da matsalar karancin barci, to, ku gaya musu cewa, dole ne su nuna jaruntaka su je wajen masana da hukumomin musamman don samun taimako.

Yin barci da kyau yana samar mana isasshen kuzari da kiyaye lafiyarmu a jiki da ma tunani. Tabbatar da lafiyar mutane a jiki da tunani duka ya aza harsashi mai kyau wajen tabbatar da samun ci gaban iyalai da zamantakewar al’ummar kasa.

Idan mun waiwaiyi baya, babban taken ranar barci ta kasa da kasa na shekarun baya-bayan nan sun hada da “A bar kananan yara su kara yin barci har awa daya”, “Yin barci da kyau don cimma buri”, “Yin barci yadda ya kamata don yin zirga-zirga yadda ya kamata” da dai makamantansu, wadanda suka nuna kyakkyawan fatan bil Adama na samun jin dadin zaman rayuwa, kiyaye lafiyar al’umma da samun ci gaba cikin dogon lokaci.

Masu karatu, bari mu yi sauye-sauye a yau! Mu magance yin barci a makare da dare, a kokarin kiyaye lafiyarmu a jiki da ma tunani. (Tasallah Yuan)