logo

HAUSA

Sin na fatan Amurka za ta nunawa duniya sahihancinta

2022-03-19 17:04:45 CRI

Kalaman da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi, yayin tattaunawarsa da takwaransa na kasar Amurka Joe Biden ta kafar bidiyo da daren jiya Jumma’a, da ya jaddada cewa, ba raya dangantakar Sin da Amurka bisa hanya madaidaiciya ya kamata kasashen biyu su yi ba, akwai bukatar su sauke nauyin dake wuyansu, don kokarin taimakawa ga shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, sun bayyana hikima gami da sanin ya kamata irin na shugaba Xi.  

Ganawar ta kasance ta biyu da shugabannin Sin da Amurka suka yi ta kafar intanet, tun bayan da suka yi shawarwari karo na farko ta kafar bidiyo a watan Nuwambar bara, inda aka samu wasu sabbi da manyan sauye-sauye a duniya bayan watanni hudu.

A wajen ganawar, Biden ya jaddada cewa, kasarsa ba ta neman yin “sabon yakin cacar baka” da kasar Sin, ba ta neman sauya tsarin kasar Sin, ba ta kuma neman kyamar kasar Sin ta hanyar inganta dangantakar kawance, kuma ba ta goyon-bayan masu kokarin balle Taiwan daga kasar Sin, kana, ba ta da niyyar tada rikici da kasar Sin. Shugaba Xi ya ce yana maida hankali sosai kan wadannan bayanai na Biden, inda kuma a cewarsa, dalilin da ya sa dangantakar Sin da Amurka take cikin wani mawuyacin hali yanzu shi ne, akwai wasu mutanen Amurka da ba su aiwatar da matsayar da shugabannin biyu suka cimma ba, kana, ba su dauki matakan zahiri don aiwatar da ra’ayin Biden ba. Amurka ba ta fahimci ainihin manufofin kasar Sin ba.

Sa’annan a nasa bangaren, shugaba Xi Jinping ya sake ambato batun “nauyin kasa da kasa” a wannan karo, inda kuma ya sake nanata matsayin gwamnatin kasar kan daidaita rikicin Ukraine. Xi ya kuma ce, a matsayin shugabannin manyan kasashe, ya dace su yi la’akari da yadda za su lalubo bakin zaren daidaita matsalolin duniya, da kuma kara la’akari da zaman lafiya da kwanciyar hankali, gami da zaman rayuwar biliyoyin al’ummar duk duniya. Xi ya ce, al’umma za su dandana kudarsa idan aka ci gaba da aiwatar da matakan takunkumi daga dukkan fannoni kuma ba tare da wani bambanci ba. Xi ya kara da cewa, abun da ya kamata a ba fifiko wajen daidaita rikicin Ukraine shi ne, ci gaba da yin shawarwari, da hana jikkatar fararen-hula da barkewar rikicin jin kai, da kuma tsagaita bude wuta tun da wuri.

A wajen ganawar, Biden ya ce yana fatan kara tuntubar kasar Sin, don hana ta’azzarar rikicin Ukraine. Kyan alkawari cikawa. Amma a lokacin da Amurka take ci gaba da neman hadin-kai da kasar Sin, sai kuma ta hada shafawa kasar Sin din bakin fenti gami da yi mata barazana da sanya takunkumi, to wannan kuma abu ne da ba shi da mafita. (Murtala Zhang)