logo

HAUSA

Adadin wadanda zazzabin lassa ta yi sanadin mutuwarsu a Nijeriya ya kai 112

2022-03-19 17:22:23 CRI

Cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Nijeriya NCDC, ta ce adadin wadanda suka mutu sanadiyyar zazzabin lassa ya kai 112, duk da matakan da gwamnati ta dauka na dakile bazuwar cutar a fadin kasar.

Wata sanarwa da NCDC din ta fitar a jiya, ta ce jimilar mutane 3,079 ne aka samu rahoton sun kamu da cutar a kasar ta yammacin Afrika tun daga watan Junairu, inda aka tabbatar da 630 daga cikinsu sun kamu.

Daga cikin adadin, 45 ma’aikatan lafiya ne da suka kamu da cutar tsakanin watan Junairu zuwa Maris. An kuma samu rahoton bullar cutar a wasu yankunan kananan hukumomi 87 na jihohi 23 daga cikin jihohi 36 na kasar.

Cibiyar ta ce tana tura kayayyakin lafiya zuwa jihohi da cibiyoyin lafiya, a matsayin wani mataki na dakile ci gaba da yaduwar cutar. (Fa’iza Mustapha)