logo

HAUSA

MDD tana kara tallafawa Mozambique don kai dauki na bala’in iskar Gombe

2022-03-18 10:59:14 CMG Hausa

Ofishin ayyukan jin kai na majalisar dinkin duniya OCHA, ya sanar da cewa, MDD da abokan hulda suna kara yawan taimakonsu wajen kai dauki ga mahaukaciyar iskar da ake kira Gombe, wacce ta afkawa yankunan gabar tekun kasar Mozambique a ranar Juma’a.

OCHA ya sanar a ranar Alhamis cewa, mahaukaciyar iskar ta haddasa mummunar ambaliyar ruwa, wanda ya yi sanadiyyar lalata dubban gidajen kwana da kayayyakin more rayuwa. Lardunan Nampula da Zambezia, su ne bala’in ya fi yiwa barna, a cewar OCHA.

Hukumar yaki da bala’u ta kasar Mozambik ta sanar da cewa, sama da mutane 400,000 bala’in mahaukaciyar iskar ya shafa, yayin da mutane 51 suka mutu kana wasu mutanen 80 suka samu raunuka. Sama da gidajen kwana 45,000 sun lalace yayin da mutane kusan 21,000 sun kauracewa muhallansu.

Ofishin hukumar ta OCHA ya sanar da cewa, dubban mutanen da suka kauracewa muhallansu sakamakon bala’in da ya faru na lokacin baya a arewacin kasar suna daga cikin wadanda lamarin ya shafa, yayin da ake da ’yan gudun hijira kimanin 9,000 da suka zo daga wasu kasashe. An fara tantance yawan bukatun da tallafin da ake da shi tun a farkon wannan mako, kana ana ci gaba da gudanar da ayyukan kai dauki da ayyukan ceto don gano wadanda suka bace. MDD da abokan hulda sun tura karin jami’ai zuwa lardin Nampula da sauran lardunan da bala’in ya shafa, kana ana bayar da fifiko wajen samar da tallafin abinci, da wurin zama da sauran kayan bukatun yau da kullum, gami da samar da ruwa mai tsafta da kayan tsaftar muhalli da kuma cibiyoyin kiwon lafiya. (Ahmad)