logo

HAUSA

MDD: Yanayin jin kai a Habasha na kara tabarbarewa

2022-03-18 09:59:31 CMG Hausa

Ofishin jami’in tsare-tsaren ayyukan jin kai na MDD, ya ce yanayin jin kai a arewacin kasar Habasha na kara tabarbarewa. Ofishin na OCHA ya ce, hakan na da nasaba da yadda cikin watanni 3 da suka gabata, aka gaza samun damar kai agaji ta hanyoyin mota, zuwa yankin Tigray dake arewa mai nisa na kasar.

Yayin da fada ke kazanta a sassan yanki, an takaita, ko dakatar da wasu ayyukan jin kai da dama a yankin na Tigray. Alkaluma sun nuna cewa, kasa da mutane 7,000 ne suka samu tallafin abinci, cikin mako daya da ya gabata, sabanin kusan mutane 870,000 da OCHA, tare da abokan huldar MDD ke da burin tallafawa a cikin makon. 

OCHA ya yi takaicin rashin samar da isasshen irin shuka mai nagarta, ga manoman yankin Tigray, gabanin faduwar damuwa nan da wata guda.

A daya hannun kuma, OCHA ya ce ana ci gaba da aikewa da kayan kiwon lafiya, da sinadaran abinci masu gina jiki zuwa Mekelle fadar mulkin Tigray. An kuma yiwa sama da dabbobi 100,000 alluran rigakafin cututtuka, duk da karancin man motaci da ake bukata domin aiki.

Ya zuwa yanzu, kimanin mutane 200,000 ne suka tserewa gidajen su, sakamakon fadan da ya barke a yankin Tigray, kuma jami’an MDD da abokan aikin su na fuskantar kalubalen kaiwa gare su. (Saminu)