logo

HAUSA

Me ya sa Amurka da ta gaza wajen yakar COVID-19 ta rika aikata laifuffuka?

2022-03-18 20:58:55 CRI

Jiya Alhamis ne, shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta yi sa-in-sa da ‘yan jarida, saboda tambayoyin da suka yi mata game da soke shirin tallafawa al’umma kan yaki da cutar COVID-19 sun fusata ta, al’amarin da ya sake shaidawa duniya cewa, a matsayinta na babbar kasa mafi karfin tattalin arziki, muradun siyasa na gaban kome a Amurka, har da rayuwar al’umma, kana, ‘yan siyasar kasar da har kullum suke ikirarin cewa, wai su ne masu fafutukar kare hakkin bil’adama, sun yi biris da kuma keta hakkokin dan Adam a fannin rayuwa.

A halin yanzu, cutar mashako ta COVID-19 na ci gaba da yin muni a Amurka, amma har yanzu babu wata mafita da mahukuntan kasar suka dauka na kawo karshen wannan matsala. Manazarta na ganin cewa, dalili kuwa shi ne, saboda yawan mace-macen ‘yan asalin Afirka da Spaniya gami da Indiyawan daji ‘yan asalin Amurka ya fi na fararen fata ‘yan kasar, ganin yadda ake yin biris da su a Amurka. Wannan abu ya sake shaida matsalar nuna wariyar launin fata da ta ki ci ta ki cinyewa a kasar.

A wajen taro na 49 na kwamitin kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya dake gudana yanzu haka a birnin Geneva, wakilan kasa da kasa sun nuna matukar damuwa kan batutuwan da suka shafi keta hakkin yara, da daukar matakan da ba su dace ba da ‘yan sanda suke yi a Amurka. A nasa bangaren kuma, zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva, jakada Chen Xu ya nuna cewa, yadda jama’a ke jin dadin rayuwa shi ne hakkin dan Adam mafi girma. A sabili da haka, ya dace ‘yan siyasar Amurka su kalli abubuwan da suka aikata da kyau. (Murtala Zhang)