logo

HAUSA

Antonio Guterres ya yi kira da a kai zuciya nesa yayin da ake tsaka da fuskantar sabanin siyasa a Libya

2022-03-18 11:13:40 CMG Hausa

A jiya Alhamis, babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya zanta ta wayar tarho, da daya daga masu da’awar kasancewa firaminista a Libya Fathi Bashagha, inda jami’an 2 suka tattauna game da halin da ake ciki yanzu haka a siyasar kasar. Guterres ya bayyana damuwa game da rikicin siyasa dake addabar Libya, lamarin da ka iya rushe nasarar da aka cimma ta wanzar da daidaito a kasar.

Da yake tabbatar da hakan, kakakin babban magatakardar MDDr Stephane Dujarric, ya ce Mr. Guterres ya yi kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki a siyasar Libya, da su kai zuciya nesa, su kuma tabbatar da daidaito. Yana mai kara jaddada matsayar MDD, ta kyamar amfani da tashin hankali, ko kalaman batanci domin cimma muradun kashin kai.

A watan Satumbar shekarar 2021 ne majalissar wakilan kasar Libya ta kada kuri’ar yanke kauna ga gwamnatin hadin kan kasa, wadda firaminista Abdul-Hamid Dbeibah ke jagoranta. Kana a ranar daya ga watan nan na Maris, majalissar wakilan ta kada kuri’ar nuna goyon baya, kana kwanaki 2 bayan hakan ta rantsar da sabuwar gwamnatin da Bashagha ke jagoranta.

Mr. Dbeibah dai ya yi watsi da halascin kuri’ar amincewar da aka kada a ranar 1 ga watan Maris, yana mai cewa, zai mika mulki ne kadai ga zababbiyar gwamnati.  (Saminu)