logo

HAUSA

Kwararre: Nasarar gudanar da gasar Olympics da Paralympics na birnin Beijing ya karfafa ruhin samar da makomar bai daya ga daukacin bil adama

2022-03-18 15:22:57 CMG

A gabar da aka kammala gasar Olympics ajin nakasassu ko Paralympic ta birnin Beijing, ta lokacin hunturu ta bana a ranar Lahadin karshen mako, Sin ta cika alkawarin ta ga duniya, ta hanyar ba da sabbin gudummawa ga harkar raya wasanni.

Masana da kwararru daga sassan duniya da dama sun bayyana gamsuwa da kokarin gasar Sin a wannan fanni, suna masu jaddada cewa nasarar gudanar da gasar ta birnin Beijing ta Olympics da Paralympics tabbaci ne ga burin da ake da shi na samar da al’ummar duniya mai makomar bai daya.

Sin ta yi iyakacin kokarin shawo kan tasirin annobar COVID-19, inda ta kai ga gudanar da gasar kasa da kasa mai matukar kayatarwa, wadda kuma baya ga cika alkawarin da Sin din ta yi, a daya hannun, hakan ya zamo muhimmiyar gudummawa mai ma’ana a fannin raya harkokin wasanni a matakin kasa da kasa, da bunkasa musayar al’adu tsakanin kasashe daban daban, da karfafa abota tsakanin al’ummun duniya.

Da yake tsokaci game da wannan batu, tsohon mai baiwa kasar Masar shawara a fannin yawon shakatawa Nasser Abdel-Aal, ya ce nasarar da Sin ta cimma a fannin shirya gasar Olympics da Paralympics a bana lamari ne a bayyane, abu ne mai karfafa gwiwa, wanda ya samar da wata dama ga sassan duniya, ta gina al’ummar duniya mai makomar bai daya .

Shi kuwa babban editan jaridar “Daily Metro Watch” da ake wallafawa a Pakistan Zahid Farooq Malik, cewa ya yi a wannan karo ma, duniya ta sake ganin kwazon Sin na nunawa duniya kyakkyawar surar duniya cikin hadin gwiwa.

Zahid Farooq Malik, ya ce yayin da Sin ke gudanar da gasannin na Olympics da Paralympic, kasar ta yayata ruhin dinkewa wuri guda, da hadin gwiwa, ta kuma ingiza muhimmin sako na muhimmancin bunkasa zaman lumana, da samar da makomar bai daya.

A cewar sa, ta hanyar wasannin, Sin ta dunkule duniya, ta kuma cimma nasarar jaddada muhimmancin gina al’ummar duniya mai makomar bai daya a fannin raya wasanni a matakin kasa da kasa.

A cewar Cavince Adhere, kwararre a fannin alakar kasa da kasa dan kasar Kenya, Sin ta samu yabo matuka daga kasashen duniya, ta hanyar shirya gasanni, duk kuwa da kalubalen annoba da aka fuskanta, ta kuma yi  rawar gani wajen tabbatar da tsaron lafiya, da kiyaye matsayin gasar yadda ya kamata.

Adhere ya kara da cewa, Sin ta nunawa duniya kimar wanzar da daidaito, da juri da kara kyautata ayyuka a cikin gida, ta hanyar wannan gasa ta Olympic, wanda hakan ya sanya Sin din zama “gida mai samar da damar bai daya ga kowa".

Shi kuwa Liu Di, farfesa a jami’ar Kyorin ta kasar Japan, cewa ya yi Sin ta gudanar da gasannin Olympics da Paralympics na lokacin hunturu, a wata gaba mai sarkakiya, kuma kaunar juna da aka nuna yayin gasar, za ta jima tana karfafa gwiwa ga hadin gwiwar bil adama, da hadin kai da ci gaban sa.

A nasa bangare, Mr. Khunying Patama Leeswadtrakul, mamba a hukumar gudanarwa ta kwamitin shirya gasar Olympic na kasar Thailand, cewa ya yi Sin ta nuna wasanni masu nishadantarwa, cikin gasar hunturu mai kunshe da tsaron lafiya, wanda hakan ya kara fito da kwazon ta na hade al’adun gargajiya, da al’adun wasannin kankara da na dusar kankara, da kuma al’adun gasar Olympic.

Gasar birnin Beijing ta 2022 ajin nakasassu, da kuma ta Olympics da ta fara gudana, ta bar alama dake da tasiri fiye da batun wasa kadai. Domin kuwa gasannin sun gwada kwazo da juriya, da karfin hali na ‘yan wasan dake da bukatar musamman, wanda hakan darasi ne da ya dace a yi koyi da su.

Daya daga manyan abubuwan mamaki ga mutane masu yawa shi ne karbar bakuncin gasar nakasassu cikin nasara. Shekaru 4 bayan samun nasarar lashe lambar zinari ta farko a gasar ajin masu bukata ta musamman ta Paralympic, ta lokacin hunturu a PyeongChang, a wannan karo Sin ta mamaye manyan lambobin gasar, inda a bana ta samu lambobin zinari a gasar alpine skiing, da biathlon, da tseren skiing mai dogon zango, da snowboarding, da curling na kan kujerun guragu, da kuma lambar azurfa a gasar hockey ta kankara.

Sin ta cimma nasarar lashe lambar azurfa a gasar hockey ta kankara ajin nakasassu karkashin tawagar kasar, duk da fara shigar tawagar gasar bai wuce shekaru 6 ba.

Lambar martabawa da Sin ta samu a wannan gasa, baya ga kasancewar ta sakamako na aiki tukuru da ‘yan wasan ta suke yi, a hannu guda hakan ya nuna irin yadda rayuwar sassan al’ummar kasar, ciki har da masu bukata ta musamman ke kara kyautata, inda su ma suke samun damammaki na bunkasar rayuwa.

Har ila yau, tawagar Sin ta wasan kwallon hockey na kankara, ta nuna irin hangen nesa, da tsara manufofi na kasar, masu taimakawa wajen dakile nuna banbanci, da rashin daidaito tsakanin al’ummun ta.

A cewar mataimakin shugaban kwamitin BOCOG Yang Shu'an, Sin ta fahimci manufar gasar Paralympic ta wuce batun lashe lambobin yabo kadai, domin kuwa gasar ta kunshi baiwa masu bukata ta musamman damar nuna kawunan su, da cimma burikan su na rayuwa.

Sin na da adadin ‘yan wasa masu bukata ta musamman da suka shiga gasar Paralympics har 96, baya ga jami’ai masu taimaka musu su 121.

Da yake tsokaci kan hakan, shugaban kwamitin shirya gasar Paralympics ta kasa da kasa ko IPC a takaice Michael Parsons, kokarin Sin na yayata wasannin da ake yi a gasar Paralympic, da kwazon kasar na samar da damammaki ga masu bukatar musamman, ya nuna cewa, kasar za ta ci gaba da yaye ‘yan wasa masu bukatar musamman dake da matukar kwarewa.

Yayin gasar ta Paralympics ta Beijing ta 2022, cikin abubuwa masu jan hankali, akwai aiwatar da matakan saukakawa masu bukata ta musamman damar gudanar da wasanni yadda ya kamata, a dukkanin cibiyoyin wasannin dake wajen birnin Beijing, da gundumar Yanqing dake arewa maso yammacin birnin, da kuma birnin Zhangjiakou na lardin Hebei.

Shi ma jami’in watsa bayanai na kwamitin IPC Craig Spence, ya ce wuraren wasa da aka samar domin ‘yan wasa masu bukata ta musamman, za su yi tasiri sosai ga sauran kasashen da za su karbi bakuncin gasar a nan gaba.

Spence ya kara da cewa, "Damar da ‘yan wasa masu bukatar musamman ke da ita, ta gudanar da wasanni cikin sauki a yayin wannan gasa da ta kammala, ta shiga kundin tarihin bajimta. Ya ce baya ga su ‘yan wasan masu bukatar musamman, damar ta kuma saukaka yanayin aikin wadanda ma ba su da bukatar musamman a yayin gasar”.