logo

HAUSA

Sharhi:Gasar Olympic ajin nakasassu ta Beijing tamkar madubi ne

2022-03-18 22:56:49 CRI

Nakassa ba kasawa ba ce, kamar yadda bahaushe kan ce.

A kwanan baya ne, aka rufe gasar Olympic ajin nakasassu ta shekarar 2022 ta Beijing, kuma a gasar ta tsawon kwanaki 9, ‘yan wasa nakasassu kusan 900 da suka fito daga kasashe da shiyyoyi 46 sun fafata a wajen gasar.

Abin lura a nan shi ne, a yayin gasar, ‘yan wasa nakasassu na kasar Sin sun yi nasarar lashe lambobin yabo da yawansu ya kai 61, ciki har da lambobin zinari 18, abin da ya sa kungiyar ‘yan wasan kasar Sin ta zo na farko ko a fannin yawan lambobin zinari da aka samu da ma ta yawan lambobin yabo da aka samu gaba daya, sabanin yadda kungiyar ta lashe lambar zinari guda daya kawai a gasar Olympic ta nakasassu ta Pyeongchang da ta gudana shekaru hudu da suka wuce, wadda ta kasance lambar zinari ta farko a tarihin kasar na halartar gasar.

Wannan saurin ci gaba da aka samu cikin shekaru hudu kawai ba ma kawai nasara ce da kasar ta samu a fannin bunkasuwar wasannin nakasassu ba, haka kuma ya shaida ci gaban kasar a fannin kare hakkin masu bukata ta musamman.

Idan ba a manta ba, a gun bikin kaddamar da gasar a ranar 4 ga wata da ya gudana a babban filin wasan kasar Sin da ake kira “shekar tsuntsu”, gomman ‘yan wasa nakasassu sun “rera” taken kasar Sin ta hanyar yin amfani da alamomi masu lalurar rashin ji, wanda ya burge kowa da kowa. Baya ga fagen wasanni, karin masu bukata ta musamman na samun nasarori a fannonin rayuwarsu na yau da kullum, kamar yadda wadanda ba su da wata nakassa suke yi, kuma hakan ba zai rasa nasaba da yadda ake kokarin kulawa da su masu bukata ta musamman da ma kare hakkinsu a kasar Sin.

Akwai masu bukata ta musamman kimanin miliyan 85 a kasar Sin, wadanda yawancinsu suke fuskantar matsaloli ta fannin rayuwa da ma kulawa da su. Don haka, a shekarar 2016, kasar Sin ta kafa tsarin samar da kudin tallafi ga masu bukata ta musamman da suke fuskantar matsalolin rayuwa da ma kudin kulawa da wadanda suke da nakassa mai tsanani. Daga shekarar 2016 zuwa 2020, tsarin ya shafi masu bukata sama da miliyan 12 da suke fuskantar matsalolin rayuwa da ma wasu miliyan 14 da suke fama da tsananin nakassa. Daga shekarar 2021 zuwa 2025 kuma, tsarin zai game dukkanin masu bukata ta musamman da ke fama da matsalolin rayuwa ko kuma tsananin nakassa.

Shugabar kungiyar masu bukata ta musamman ta kasar Sin malama Zhang Haidi ta taba bayyana cewa, “Masu bukata ta musamman suna iya kama sana’o’i iri iri kamar yadda wadanda ba sa fama da wata nakassa suke yi.” Hakan abin yake, a nan kasar Sin masu bukata ta musamman suna da ‘yancin samun ilmi da guraben aiki kamar takwarorinsu wadanda ba su da nakassa. Alkaluman da aka samar sun yi nuni da cewa, daga shekarar 2016 zuwa ta 2020, gaba daya akwai masu bukata ta musamman da suka ci jarrabawar shiga jami’o’i, karuwar kaso 50.11% kwatankwacin na shekarar 2011 zuwa ta 2015, baya ga kuma wasu karin miliyan 1.81 da suka samu guraben aikin yi a cikin garuruwa. Ban da haka, masu bukata ta musamman kimanin dubu 400 ne su kan samu damar shiga kwasa-kwasai na horar da fasahohin sana’o’i da gwamnatin kasar ta dauki nauyi

A gasar Olympic ajin nakasassu ta lokacin hunturu ta Beijing, yadda aka samar da wani yanayi na kawar da matsaloli ga dukkan ‘yan wasa nakasassu na kasashe daban daban ya burge kowa, kuma hakan wani bangare ne na yadda kasar Sin ke kokarin kawar da matsaloli ga masu bukata na musamman a kasar, inda aka gyara kimanin kashi 38% na ban daki dake kauyuka da unguwannin kasar, don masu bukata ta musamman su samu saukin yin amfani da su. Baya ga haka, an kuma gyara jiragen kasa da motocin bas don saukaka musu……

Yadda aka samar da tabbaci da ma dada kyautata rayuwarsu ya zama tushen yadda masu bukata na musamman na kasar Sin ke kokarin shiga harkokin wasanni da ma sauran fannonin zamantakewar al’umma. Gasar Olympic ajin nakasassu ta Beijing tamkar madubi ne, wadda ta shaida ci gaban harkokin wasanni na masu bukata ta musamman, da ma ingantuwar yanayin da suke ciki. Kamar yadda mataimakin shugaban kwamitin shirya wasannin Olympic na lokacin hunturu na Beijing, Mr.Yang Shu’an ya fada, “sakamakon ci gaban tattalin arziki da zaman al’umma, an kara kulawa da nuna goyon baya ga harkokin wasanni na masu bukata ta musamman, tare kuma da yadda su kansu suke kokari, duk wadannan su ne suka taimaka mana wajen samun nasarar.” (Lubabatu Lei)