Hadarin matakin Amurka na sayarwa Taiwan makamai
2022-03-17 16:20:37 cri
Masharhanta da dama na ci gaba da ganin baiken alaka, da cudanyar dake wakana tsakanin Amurka da yankin Taiwan na kasar Sin, inda sau da dama, Amurka ke sayarwa yankin na Taiwan makaman aikin soji, matakin da ya yi matukar sabawa dokokin kasa da kasa, da ka’idojin da kasashen duniya suka amincewa, da yarjejeniyoyin da ita kanta Amurka ta kulla tare da bangaren kasar Sin.
A lokuta mabanbanta, Sin ta sha nuna rashin amincewarta da wadannan matakai na tsoma hannu cikin harkokin gidan ta, matakin da ka iya haifar da yanayi na rashin jituwa tsakanin Sin da Amurka, da gurgunta alakar sassan biyu, tare da haifar da zaman dar dar a zirin Taiwan.
Ko da a baya bayan nan ma, wasu rahotanni sun nuna yadda Amurka ta sanya hannu kan wasu kwangiloli na sayarwa Taiwan wasu na’urorin sadarwa na aikin soji, wadanda kudin su ya kai kimanin dalar Amurka miliyan 245. An kuma bayyana cewa, yankin na Taiwan zai karbi na’urorin a watan Satumbar 2025, a wani bangare na zartas da shirin Amurkar na sayarwa Taiwan makamai da sassan suka amincewa tun a watan Disambar shekarar 2020.
Ko shakka babu, abu ne mai ban mamaki, yadda sau da yawa Amurka ke bayyana amincewarta da manufofin kasar Sin, na kasancewar Sin daya tak a duniya, kuma kasa mai ikon mulkin kai da dukkanin yankunanta. A hannu guda kuma, take aiwatar da irin wadannan matakai na sayarwa Taiwan da makamai ta bayan fage. Hakan tamkar tufka da warwara ne. Kuma mataki ne mai hadarin gaske, wanda zai haifar da babbar baraka tsakanin Amurka da Sin, zai kuma ci gaba da zubarwa Amurka da kima a idanun duniya, duba da matsayinta na babbar kasa mai fada a ji, amma kuma a lokaci guda, mai saba alkawuran da ta dauka, tare da rura wutar sabani, da rikici, da ta da zaune tsaye! (Mai fassara: Saminu Hassan)