logo

HAUSA

Akalla mutane 19 ne suka mutu a wani harin ta'addanci a jamhuriyar Nijar

2022-03-17 19:39:07 CRI

Majiyar tsaron Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa, a kalla mutane 19 da suka hada da 'yan sanda biyu ne suka mutu a yammacin ranar Laraba, a wani harin ta'addanci da aka kai kan wata motar safa da ta taso daga kasar Burkina Faso zuwa garin Tera dake yammacin jamhuriyar Nijar.

Bayanai na cewa, maharan da ke kan Babura, sun tare motar bas din ce a kusa da kauyen Petel kole da misalin karfe 1:00 na rana agogon wurin, inda suka budewa fasinjojin dake cikin motar wuta tare da kona motar.

Sai dai jami'an tsaron jamhuriyar Nijar sun yi nasarar fatattakar 'yan ta'addan, inda suka fantsama ciki da kewayen yankunan

Yankin da aka fi sani da "iyakoki uku" wato kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso, a ‘yan shekarun baya-bayan nan dai, ya zama tungar kungiyoyin 'yan ta'adda da ke kai munanan hare-hare a dukkan bangarorin biyu na kan iyakokin kasar, inda suke kaiwa sojoji da fararen hula hari.