Kasar Sin na kara karfafawa duniya gwiwa wajen farfado da tattalin arziki
2022-03-17 20:27:13 CRI
A wajen taro na musamman da kwamitin tabbatar da ci gaban harkokin hada-hadar kudi na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya a jiya Laraba, an maida martani daya bayan daya kan wasu batutuwan da suka jawo hankalin kasuwannin kasar, ciki har da raya tatttalin arziki daga manyan fannoni, da batun kadarorin gidaje, da sauransu. Manazarta da dama sun nuna cewa, an kira taron ne cikin lokaci, wanda ya aike da wani sako a fili cewa, gwamnatin kasar Sin na bakin kokarinta wajen tabbatar da raya tattalin arziki bisa hasashen da aka yi, da neman jarin waje da samar da ci gaba yadda ya kamata, al’amarin da ya baiwa masu zuba jari na kasashen ketare kwarin-gwiwa sosai.
Kasuwannin hada-hadar kudi a kasar Sin sun fuskanci babban matsin lamba a wasu watannin da suka gabata, inda aka gano cewa, shugabannin kasar sun yi tunani da nazari mai zurfi game da wahalhalun da tattalin arzikin kasar ke fuskanta a halin yanzu, haka kuma suna da yakinin cewa, za’a shawo kan wadannan kalubalolin.
Tun daga babban taro kan ayyukan tattalin arzikin kasar da aka shirya a karshen bara, har zuwa rahoton aikin gwamnatin da aka gabatar a kwanan baya, raya tattalin arziki yadda ya kamata shi ne aka ba muhimmanci. Haka kuma a wajen taro na musamman da kwamitin tabbatar da ci gaban harkokin hada-hadar kudi na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya a jiya Laraba, an sake jaddada cewa, ya dace a tabbatar da dorewar manufofin tattalin arziki.
Duk wadannan abubuwa sun shaida cewa, tsarin hada-hadar kudi yana kara taimakawa ga ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, da bada tabbaci ga raya tattalin arzikin kasar na dogon lokaci kuma ta hanyar da ta dace, kana, farfadowar tattalin arzikin kasar Sin yana kara karfafawa duk duniya gwiwa. (Murtala Zhang)