logo

HAUSA

An yi kira ga kasashen Afirka da su aiwatar da matakan cin gajiya daga kasuwannin zamani

2022-03-16 10:54:22 CMG

Mataimakiyar kwamishina a hukumar zartaswar tarayyar Afirka Monique Nsanzabaganwa, ta yi kira ga mahukuntan nahiyar, da su bullo da wasu tsare tsare, da za su ingiza cin gajiyar kasashen su daga kasuwannin zamani masu kunshe da fasahohin sadarwa.

Uwargida Nsanzabaganwa ta ce, ya kamata kasashen nahiyar su yi amfani da damar dake akwai, karkashin kasuwannin zamani masu kunshe da na’urori daban daban, wajen bunkasa damar saye da sayarwa, da fannin ba da hidima tsakanin kasashen nahiyar.

Kalaman jami’ar na zuwa ne, yayin da kasashen Afirka suka bi sahun takwarorinsu na sassan duniya, wajen gudanar da bikin ranar masu sayayya ta duniya karo na 39, wanda ake gudanarwa a duk ranar 15 ga watan Maris.

A bana, taken bikin shi ne "Samar da damar bai daya na cin gajiya daga cinikayya ta fasahohin zamani". Game da hakan, Nsanzabaganwa ta ce dandazon matasan da Afirka ke da su, na kara shiga a dama da su a sauye sauyen fasahohin sadarwa na duniya, don haka ya zama wajibi masu tsara manufofi a nahiyar su yi amfani da wannan dama, wajen kirkiro dabarun baiwa matasan nahiyar damammaki cin gajiya daga sauyin. (Saminu)