logo

HAUSA

Biri Ya Yi Kama Da Mutum

2022-03-16 16:27:22 CRI

Tun bayan da kasar Rasha ta bankado wasu muhimman takardu, da hotuna, gami da shaidu na zahiri game da dakunan binciken kwayoyin halittun Amurka dake kasar Ukraine, bangaren Amurka ya yi amfani da kalmar wai "bayanan karya" don gyara abubuwan da suka gabata, wanda zai yi matukar wahala ta gamsar da al’ummar duniya.

A ranar 11 ga wata ne, kwamitin sulhu na MDD, ya gudanar da wani taro, don tattauna batun tsaron kwayoyin halittun dake dakunan gwajin da Amurka ta kafa a kasar Ukraine. Yayin da kwamitin na MDD ke kokarin neman karin bayani kan wannan batu, sai ita kuma wakiliyar din din din ta kasar Amurka a MDD Linda Thoms-Greenfield ta bayyana cewa, wai kasar Sin tana yada labaran karya don tallafawa kasar Rasha.

Sanin kowa ne cewa, Amurka a ko yaushe tana ambato “gaskiya a baki”. Amma a zahiri lamarin ba haka yake ba. Masu bibiyar al’amuran yau da kullum na cewa, Idan har Amurka ta ce, wannan “bayanan karya ne”, to me ya sa ba ta ba da cikakkun bayanai don tabbatar da cewa ba ta da laifi? Ina tsabar kudi har dala miliyan 200 din da Amurka ta kashe? Kuma wane bincike Amurkar ta gudanar, kuma a kan wadanne cututtuka? Wadannan duk tambayoyi ne da duniya ke bukatar amsoshin su daga bangaren Amurka. Kuma rashin bayar da gamsassun amsoshi, na iya tabbatar da cewa, akwai wani abu da Amurka ba ta son duniya ta sani game da wadannan dakunan bincike. Akwai lauje cikin nadi

Ana haka ne kuma, sai aka wari gari shi ma ofishin jakadancin Amurka a Ukraine, ya goge duk wasu bayanan da suka shafi wannan batu a shafinsa na intanet. Tambaya a nan ita ce, wai me mahukuntan Amurka suke kokarin boyewa? Me ya sa Amurka ke adawa da kafa tsarin bincike na bangarori da dama game da yarjejeniyar makamai masu guba ta shekaru 20 da suka gabata?

Idan Amurka tana son jefar da kwallon mangoro da huta da kuda, ya kamata ta bude wadannan dakunan gwaje-gwaje na kwayoyin halittu da sauran irin wadannan dakunan gwaje-gwajenta kamar yadda ga tawagar masanan lafiyar kasa da kasa don gudanar da bincike a kansu. Idan ba haka ba, to, Wannan na kara tabbatar da cewa, Biri dai ya yi kama da mutum. (Ibrahim Yaya)