logo

HAUSA

Jakadan Sin a Nijar ya gana da shugaban kamfanin dillancin labarai na jamhuriyar Nijar

2022-03-16 11:34:07 CMG

A jiya Talata ne jakadan kasar Sin a jamhuriyar Nijar Jiang Feng ya gana da shugaban kamfanin dillancin labarai na Nijar malam Daratu. Yayin ganawar tasu, sassan biyu sun zarfafa tattaunawa game da alakar Sin da Nijar, da batun karfafa hadin gwiwar sadarwa tsakanin kasashen biyu.

Jakada Jiang ya ce, Sin da jamhuriyar Nijar na da alaka ta kawance, suna kuma gudanar da hadin gwiwa a sassa masu yawa, tare da cimma manyan nasarori. Har ila yau, suna gudanar da musaya da hadin gwiwa a fannin watsa labarai, wanda hakan ya zamo muhimmin bangare na kawancen su.

Jami’in ya bayyana fatan ganin kamfanin dillancin labarai na Nijar, ya ci gaba da yayata rahotanni game da nasarori, da ci gaban da ake samu karkashin inuwar hadin gwiwar kasashen 2.

A nasa tsokaci kuwa, shugaba Daratu, godewa bangaren kasar Sin ya yi, bisa kwazonsa na tallafawa jamhuriyar Nijar. Yana mai cewa, kamfaninsa zai ci gaba da yada rahotanni da suka jibanci kasar Sin, da yaukaka hadin gwiwa da kafofin watsa labarai na Sin, ciki har da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, don ba da gudummawar raya abota da hadin gwiwa tsakanin Nijar da Sin. (Saminu)