Ma'auni biyu da Amurka da kasashen yammacin duniya suke amfani da su kan 'yan gudun hijira yana nuna girman kai da son zuciyarsu
2022-03-16 21:43:35 cri
“A kasar Syria, duniya ta ga yadda aka rika kisan kiyashi da aka yiwa wata al’umma baki daya, wanda kasashen yamma da dama suke da hannu a ciki, amma a kasar Ukraine, dukkan kasashen yammacin duniya na kare jama’arta.” Kwanan nan, jami’in kwamitin shawarwarin na Syria Anas Al-Abdah, ya bayyana yayin wata hira da ‘yan jarida cewa, bai ji irin "ma'aunai biyu" da kasashen yamma suke nunawa ba.
A jiya ne, ake cika shekaru 11 da tayar da rikicin kasar Syria. Amma kasashen yamma sun nuna matukar tausayawa 'yan gudun hijirar na Ukraine, idan aka kwatanta da kokarin da suka yi na hana 'yan gudun hijira daga wasu wurare, ciki har da Syria shiga kasashensu cikin 'yan shekarun nan. Har ma wasu 'yan siyasa da kafofin watsa labaru na kasashen yammacin Turai suna amfani da launin fata, kabilanci, da sauransu a matsayin ma'auni, inda suka fi martaba 'yan gudun hijirar Ukraine fiye da na yankunan Gabas ta Tsakiya da na Afirka
Kalaman da suka fallasa tsatsauran ra'ayi na kabilanci da kuma girman kansu na "Dora muhimmanci kan Turai da Amurka”. Suna daukar ma’auni biyu kan ‘yan gudun hijira da aikin jin kai.
Kamar yadda wata 'yar majalisar dokokin Turai Clare Daly ta ce, kawai suna ambatar Ukraine ne, amma ba a maganar Afganistan, domin Amurka ce ta mamaye Afghanistan.
Hakika Amurka ta taka mummunar rawa tun daga yakin Afganistan zuwa yakin Syria har da rikicin Ukraine. Kuma batun wanda aka damu da wanda ba a damu da shi ba, ba shi da alaka da adalci, gaba daya ya samo asali ne sakamakon magudin hadin gwiwa na 'yan siyasar Amurka da kafofin yada labaran kasar. A ganinsu, ko ‘yan gudun hijira daga Gabas ta Tsakiya ko daga Ukraine, dukkansu wani makami ne kawai na neman cimma muradun siyasarsu da kuma nuna danniya ko babakere. (Mai fassara: Bilkisu)