logo

HAUSA

Karuwar jarin waje a kasar Sin alama ce ta imanin da kamfanonin waje ke da shi kan kasuwar kasar da ci gabanta

2022-03-15 19:14:46 CRI

Wasu alkaluma da ma’aikatar kula da harkokin kasuwanci ta kasar Sin ta fitar, sun nuna yadda jarin waje da kasar Sin ta yi amfani da shi tsakanin watannin Janairu da Fabarairun bana ya karu da kaso 37.9 bisa dari, har ya kai kudin kasar yuan biliyan 243.7.

Wannan dai kyakkyawar alama ce dake nuna yadda kamfanonin kasashen waje ke kara imani da kasuwar kasar Sin.

Duk da irin kalubale dake ci gaba da addabar duniya, kasuwar kasar Sin ta kasance mai kwari dake taimakawa kamfanonin kasashen waje.

Wannan kuma ba zai rasa nasaba da yadda a ko da yaushe kasar ke kokarin fadada bude kofarta ga kamfanonin na waje ba. Har ma da kyautata manufofinta na jan hankalin masu zuba jarin. Har ila yau, yana da nasaba da ci gaban da kasar ke samu ta bangarori da dama kamar daga ababen more rayuwa, zuwa kwanciyar hankali da zaman lafiya da kyautatuwar rayuwar jama’a. Domin kuwa idan babu wadannan, to harkokin kasuwanci ba za su gudana yadda ake bukata ba.

Ko a baya-bayan nan yayin taruka majalisar wakilan jama’ar kasar Sin da ta majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar, an yanke shawarar kara kyautata tsarukan jan hankalin jarin waje da kuma sake nazarin wasu bangarori da a baya kamfanonin waje ba su da damar zuba jari, har ma da kyautata tsaruka ta yadda za a kara basu damarmaki iri daya da takwarorinsu na cikin gida.

Wannan ya nuna, manufofi da matakan kasar Sin a aikace. Wato bude kofar da take fada, lallai tana yinsa, kuma tana martaba kamfanonin da jarin waje. Lamarin da zai kyautata huldar bangarori da dama da kasa da kasa har ma da habakar tattalin arzikin duniya, samar da gurben ayyukan yi da ma uwa uba wadata da zaman lafiya tsakanin al’umma.

Bugu da kari, karuwar yawan jarin, shaida ce cewa kamfanonin waje na jin dadin gudanar da harkokinsu a kasar Sin, kuma kasar da al’ummarta na maraba da su. Haka kuma shaida ce cewa, kasar ta yaki talauci, kuma al’ummarta na cikin wadata. (Fa'iza Mustapha)